✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Illar cin mutuncin mutane (1)

Gabatarwa: Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ku bi Allah Madaukaki da takawa a cikin magana da aiki. Ku yi maSa takawa bisa tawali’u da…

Gabatarwa: Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ku bi Allah Madaukaki da takawa a cikin magana da aiki. Ku yi maSa takawa bisa tawali’u da bin umarninSa safe da maraice, kuna masu tabbatar da girma da daukaka da fiffiko da kamalarSa. “Kuma wanda ya bi Allah da takawa, Allah zai kankare masa munanan ayyukansa, kuma Ya girmama masa sakamako.” (k:65:5).
Ya ku Musulmi!  A yayin da duniya ke fama da fitintinu masu yawa, jere da juna, take fama da munanan bala’o’i marasa iyaka, wadanda suke girgiza zukata suka shallake tunani da hankulan jama’a, sai ga zamani ya zo da wani sabon abu da ke bata tunani ke raunana tunanin zababbu da gama-garin jama’a, yana bijiro da al’umma zuwa ga rarrabuwa da rugujewa, yana kekketawa da yayyaga hadin kan jama’ar Musulmi da zaman lafiyarta.  Al’umma ba ta ji zafi ba, face saboda aukuwarsa, jama’a da daidaikun mutane ba su gushe ba, face wannan abu yana kekketa su yana karya su, yana jefa su cikin fushin zubar da jini.
Wannan abu – Allah Ya tsare ku – shi ne cin mutuncin mutane da bata martabarsu da tuhumar barrantattu daga cikinsu da niyyar cin zarafinsu. Hakika wannan abin ki ne, kuma kaiton yin haka, Allah wadaran wannan abin zargi da wawaye suke riko da shi, hali ne da ke kaiwa ga watsa kazafi da kiren-karya da kalamai masu jawo fasadi a tsakanin Musulmi, ya kawo juya baya ga juna da kaurace musu. Hakan na lalata zamantakewa ya jawo kirkirar karya a kan mutum ba kunya ba tsoro, ba don komai ba, sai don a zubar da mutuncin wani haka kawai, kuma a haifar da cutarwa marar iyaka da za ta daidaita zaman jama’a ta girgiza tushen zaman al’umma.
Saboda wadannan miyagun abubuwa da wannan dabi’a ke jawowa na dagula al’amura da bata zaman lafiya, sai gargadi mai karfi da tattalin  narkon azaba mai tsanani ya zo a cikin Alkur’ani da Sunnah kan munin makomar duk mai kiren-karya yana watsawa: “Kuma wadanda suke cutar muminai maza da muminai mata, ba da wani abu da suka aikata ba, to, lallai sun dauki kiren-karya da zunubi bayyananne.” (k:33:58).
Daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Riba tana da matakai ko nau’o’i har saba’in. Mafi saukinta shi ne misalin mutum ya yi zina da mahaifiyarsa. Kuma lallai mafi girman riba, shi ne mutum ya rika cin mutuncin dan uwansa.” Bazzaru ya ruwaito shi a cikin Musnad dinsa sai Ibn Abu Shaiba a Musnaf dinsa.
Allahu Akbar! Me ya kai girman mutuncin Musulmi? Me ya kai daukaka da karimcinsa? Domin haka ne shari’a ta tsare shi kada a zagi mutum kada a fada masa mummunar magana kada a auka wa mutincinsa, kada a soke shi kada a yi masa kazafi. Kai kiyaye mutunci, mafi kyan abin da ake nema ne, kuma mafi girman manufofin shari’a kamar yadda ma’abuta ilimi irin su Shadabi da wadansu suka bayyana.
Ya ku muminai! Bin aibobin mutane da al’aurorinsu don gano nakasunsu da gazawarsu da kazantarsu mummunar hanya ce mai halakarwa. dabi’a ce ta mutanen da ake zargi kuma kazanta ce, kuma ta saba wa shari’ar Allah Madaukaki da shiriyar ManzonSa (SAW) wanda yake cewa: “Albarka ta tabbata ga wanda ya shagaltu da laifuffukansa daga laifuffukan mutane.” Bazzaru ya ruwaito a Musnad dinsa sai Baihaki a Shu’ubarsa.
Wani magabaci yana cewa: “Mun riski magabatan kwarai ba su ganin ibada ta takaita a kan Sallah da Zakka kawai, a’a suna ganin ta hada da kamewa daga taba mutuncin mutane.” Kuma Malik bin Dinar (Allah Ya yi masa rahama) ya kasance yana yawan cewa: “Ya ishi mutum zunubi a ce bai kasance salihi ba, saboda yana aukawa ga cin mutuncin mutane.”
Kuma mafi muni daga cikin cin mutunci shi ne a rika kazafi kiri-kiri a soki mutum a bata shi a ce ba haka yake nufi ba a zuciyarsa, a tuhumi niyyarsa da manufarsa. A kutsa cikin dukkan siffofi na gaibi da ke cikin zuciyarsa a yi masa kazafin aibubbuka da barna da babu wanda ya san hakikaninsu ban da Allah Madaukaki. Kuma a yi ta watsawa da yayata wadannan abubuwa ta hanyar kiyayya da rudin mutane a kawata kalmomi na karya a basar da jahilai a watsa sharruruka. Ina abin da ya kai wannan zama abin bakin ciki, tir da wannan abin bakin ciki!
Kuma karin abin bakin ciki da ke cikin wannan muguwar dabi’a ta keta rigar mutuncin mutane, shi ne, yadda ire-iren wadannan karairayi suke zama tamkar gaskiya a wurin mutane. Su zamo su ne daidai, su ne gaskiya.
Ku ji tsoron Allah! Ku ji tsoron Allah! Ba yadda za a yi haka ya zama gaskiya, wannan ba wani abu ba ne, face jahilci da mugun zato da suke haifar da aibu da gadar da zunubi. Masu yin haka Allah Ubangijin talikai Ya siffanta su da cewa: “Ba mu zato, face zato mai rauni, kuma ba mu zama masu yakini ba.” (k:45:32).
Kowane lafazi za a taskace shi a cikin littattafan ayyukanmu domin Ranar Hisabi, a cikinsa za mu ga aikin sharrin da muka furta da bata wani da muka yi a cikin lafazi da labari an rubuta su lafazi-lafazi.
Ya ’yan uwa a cikin imani! Ana yin haka ne alhali miyagun abubuwa suna karuwa, munanan ayyuka suna dada yaduwa, cin mutunci ya zama babban abin ado a tsakanin al’umma. Malamanta sun zamo abin dariya, wanda yake cin mutuncinsu ya zama hazaki abin koyi a tsakanin mutane, ya zama tauraro, saboda yana tozarta lamarinsu, yana bata su ta kafafen sadarwa na zamani!
Duk inda ka juya abin da za ka gani, shi ne suka da zagi da soki burutsu da cin dunduniya ta amfani da alkaluma a yada dafin mujirimanci da harsuna masu guba a ci mutuncin mafifitan cikin al’umma, barrantattu da salihai da masu tsarkinsu, wandanda suke rayuwa domin gyara da maganin cututtukan al’umma!
Hakika mai tsira da amincin Allah ya fadi a cikin mashahuriyar hudubarsa a Ranar Arfa cewa: “Lallai jininku da dukiyarku da mutuncinku haramun ne (katangaggu ne) a tsakaninku, kamar yadda wannan rana taku take (da martaba) a wannan gari naku, a wannan wata naku (masu alfarma).” Kuma (SAW) ya ce: “Kowane Musulmi haramu ne a kan dan uwansa Musulmi ya taba jininsa ko dukiyarsa ko mutuncinsa.” Muslim ya ruwaito.
Imam Ahmad (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Ban taba ganin wani yana magana a cikin mutane ba (yana cin mutuncinsu), face (mutuncinsa) ya zube.”
Shaihul Islam Ibn Taimiyya (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Magana kan mutane wajibi ne ta kasance bisa ilimi da adalci ba da jahilci da zalunci ba. Kuma auka wa mutuncincu ya fi satar dukiyarsu muni.”
“Ya mai keta mutuncin mutane mai yanke, Hanyoyin kauna da soyayya, za ka rayu ba abin mutuntawa ba.
Da ka kasance ’yantacce daga tsatso mai girma,
Ba za ka kasance mai keta mutuncin Musulmi ba.”
Don haka ya ku ’yan uwa a cikin imani! Lallai mai kutsawa a cikin mutuncin Musulmi, kuma mafi muni da kebantar girman masu karkata, shi ne mai cin mutuncin shugabannin Musulmi da malamai da masu gyara. Halinsa shi ne juya wa Allah baya da bijire maSa, mai komawa zuwa ga tsanani, bai san ya yi godiya da shukura ga ma’abucin falala ba, balle ya san kima da matsayinsa.
Hakika an wayi gari wadansu mutane musamman saboda samuwar sababbin hanyoyin sadarwa, sun zamo ba su da sukuni, ba su da hakuri, face sun kekketa mutuncin mutane da munanan kalamai da zunde da tuhume-tuhume. Tir da manufa da burinsu. Suna rubuta zur da alkalumansu, suna boye gaskiya. Da haka tunaninsu ke umartarsu domin su samu damar wargaza hadin kan al’ummar Musulmi da muminai ta hanyar rubuce-rubucen son zuciya da bin son rayukan kungiyoyi da mazhabobinsu, ba su yin aiki face ga wadansu kungiyoyin asiri da burinsu shi ne wargaza hadin kai da zaman lafiyar al’ummar Musulmi.  
Ya ku masu keta mutunci domin ganin bayan Musulmi da kawo karshensu! Ku nisanci wadannan miyagun abubuwa masu fusatarwa, ku ciru daga wadannan abubuwa masu halakarwa, ku yi kwadayi zuwa addini ta hanyar neman tsira da salama gabanin aukuwar mutuwa mai zuwa afke da nadama: “Kuma ba domin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, a cikin duniya da Lahira. Lallai ne, da azaba mai girma ta shafe ku a cikin abin da kuka kutsa da magana a cikinsa.” (k:24:14).