✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ilimin Kwanfuta ya taimaka mani wajen kwarewa a kida da waka – Garkuwan mawaka

Aminiya ta tattauna da wani matashin mawaki mai suna Adamu Iliyasu, dan asalin Jihar Kano, inda ya bayyana yadda ya fara waka, da kuma dalilin…

Aminiya ta tattauna da wani matashin mawaki mai suna Adamu Iliyasu, dan asalin Jihar Kano, inda ya bayyana yadda ya fara waka, da kuma dalilin da ya sa ya shiga harkar waka, da kuma yada ilimin Kwanfuta ya taimaka masa wajen kwarewa wajen kida da waka.

 

Aminiya: Ka gabatar mana da tarihinka a takaice?

Sunana Adamu Iliyasu Garkuwan Mawaka. An haifeni a Jeli da ke Qaramar Hukumar Tudun Wada, Jihar Kano. Na yi Firamare a garin Jeli, wato Jeli Primary School, sannan na yi Sakandarin gwamnati ta Tudun Wadar Xankadai. Dagan an sai ban ci gaba da karatu ba, amma yanzu haka na kusa komawa makaranta.

Aminiya: Me ya ja hankalinka ka shiga harkar waka?

Abin day a ja hankalina na fara waka shi ne tun ina karami na fara rubuta waka saboda na kasance mai matukar ra’ayin waka tun lokacin. Tun ina rubutawa ina ajiyewa har na fara rubutawa ina rairawa. Kuma na samu nasarar hada waka da kida ne tare saboda irin basira da hikima da Allah Ya bani, musamman saboda irin ilimi da nake da shi ilimin kwamfuta. Gaskiya Kwamfuta ta taimaka mani wajen samun sauki. Da yake waka na fara, kuma na dade ina harkar kafin na fara kida. Abin da na lura shi ne yadda hada sautin ke da sauki. Kuma na kasance ina sha’awar yin kida. Da na lura cewa ilimin da nake da shi na Kwamfuta, sai na ga lallai nima zan iya domin na iya Kwanfuta sosai. Koda na fara, sai na ga ashe zan iya. Sai kuma Allah Ya saukake mani lamarin. Cikin ikonSa sai gashi yanzu na shahara a matsayin mawaki, kuma makidi.

Aminiya:  Yaushe ka fara waka?

Na fara waka ne a shekarar 2002. Kuma da waka na fara kafin daga baya na fara kida, sannan na ci gaba da yin duka tare. Sannan kuma zuwa yanzu na yi wakoki a akalla guda 20. Ina da burin zama fitaccen mawaki a fadin duniya. Kuma yanzu idan ka kirga, za ka cewa ya kwashe kusan shekara 15 ke nan ina waka. Ka  ga ke nan an dade ana yi. Da yake dai daukaka ta Allah ce. Amma ko yanzu AlhamdulilLahi. Duk na shiga sai ka ji ana ga Garkuwan mawaka. 

Aminiya: Akwai rufin asiri a wannan harkar ta kida da waka?

Gaskiya mun gode wa Allah. Wannan sana’ar akwai rufin asiri mai yawa. Ta dalilin wannan sana’a gaskiya na san mutane da yawa, musamman manya manyan mutane wadanda bai cin wannan sana’a ba zan iya ganinsu ba.  Kuma ta sanadiyar wannan harka, na samu daukaka ta inda ban zata ba. Sunana ya yadu sosai, ko ina ana jin wakoki, kuma ina yi wa manyan mawaka kida. Wannan ya sa na samu suna. Ka ga ko wannan ma kadai ai rufin asiri ne. Sannan kuma an samu abin duniya ma ba laifi. Don haka ina godiya ga Allah. Kuma ina addu’ar Allah Ya kara min daukaka. 

Aminiya: Ko kana da maigida a wannan harkar?

Ina da maigida, amma a bangaren kida ba waka ba. Saboda ita waka kamar yadda na fada maka, na dade ina rubutawa, amma sai daga baya na rairawa. Kusan zan iya cewa baiwa ce kawai Allah ya min. na taso ne kawai nag a ina yin waka. Kuma babu irin wakar da bana iya yi. Kawai dai Allah ne Ya dafa mani cikin ikonSa. 

Aminiya: Mene ne kiranka ga mawaka?

Kirana ga mawaka manyanmu da yaranmu shi ne mu dau waka sana’a, kuma mu san cewa wannan wata hanya ce mafi sauki ta isar da sako. Don haka ina kira garemu da mu tsaftace sana’ar, musamman a matsayinmu na masu fadakarwa. A matsayinmu na masu fadakarwa, dole duk aka ganmu, a ga alamar fadakarwa din da muke magana. Kuma mu kyautata niyyarmu. Kuma mu so juna, kada mu bari karamar matsala ta raba mu.

Aminiya: Mene ne kiranka ga jama’a masoya?

Kirana ga masoya masu saurarenmu shi ne idan sun ji mun yi kuskure kamata ya yi su rika sanar da mu. Sannan kuma su daina matsayin ’yan iska, domin ta hanyar waka, ana iya aika sako da yawa. Babban burinmu shi ne mu nishadantar da ku kuma mu fadakar da ku. Ba mu da burin bata muka rai ko kadan. A kulluma tunaninmu shi ne ya za mu mu birge ku. To idan ba ku aiko mana da sakonnin inda kuka mun yi kuskure, ba za mu sani ba ballantana mu gyara. Don haka maimakon ku rika maganar kuskurenmu a waje, gara ku mana magana, mu kuma za mu gyara.