Matakan da za ka bi idan kana so ka zama mai adalci:
Mataki na farko ya kunshi dawowa ga Allah, wato yarda da shirin da Ya yi domin ceton dan Adam. Mun yi karatu a makon jiya daga cikin Littafin 2Korinthyawa 5 : 17, wanda yake cewa: “Idan fa kowane mutum yana cikin Kiristi, sabon halitta ne; tsofaffin al’amura sun shude; ga kuwa, sun zama sababbi.” Matakin farko shi ne:
Haduwa da Yesu Kiristi ta wurin ba da gaskiya gare shi, wannan ya zama kamar dole ne, domin maganar Allah na cewa cikin Littafin Romawa 3 : 19 – 23 – 26, “Mun sani dai, iyakar abin da shari’a ke fadi, tana fadi ga wadanda ke karkashin shari’a, domin bakin kowa shi kwabu, a komo da dukan duniya karkashin hukuncin Allah: gama ta wurin ayyukan shari’a ba mai rai da za ya barata a gabansa ba; gama ta wurin shari’a ake sanin zunubi. Amma yanzu ban da shari’a wani adalci na Allah ya bayana, Attaurat da Annabawa kuwa suna shaidarsa, wato adalcin Allah ta wurin ban-gaskiya cikin Yesu Kiristi ke nan zuwa ga dukan masu ba da gaskiya, gama ba maraba; da yake dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah; bisa ga alherinsa an barata a yalwace ta wurin fansa da ke cikin Yesu Kiristi: wanda Allah ya ayyana abin fansa ne, ta wurin ban-gaskiya, bisa ga jininsa, domin a bayyana adalcinsa, inda ya bar lura zunubai marigaya cikin jimrewar Allah; domin bayyanuwar adalcinsa a cikin zamani na yanzu; domin shi da kansa shi bara ta, ya kuma baratar da wanda yake da ban-gaskiyac ikin Yesu.”
Sai mu sani fa cewa idan dai ta wurin ayyukan shari’a ne, babu wani mai rai da za ya barata a gaban Allah. Idan aka tattara adalcinmu na mutuntaka gaba daya, ba za a taba gwada shi da adalcin Allah ba. A gaban Allah dukan kyawawan ayyukanmu muddin idan ba a cikin Kiristi Yesu ba, suna nan kamar tsumma da ya gama rubewa a gaban Allah, ba ya da amfani ko kadan. Idan muka duba cikin Littafin 2Koirnthyawa 5 : 18 – 21, maganar Allah tana cewa: “Amma abu duka na Allah ne, wanda ya sulhunta mu ga kansa ta wurin Kiristi, har ya ba mu hidima ta sulhu; wato, Allah yana cikin Kiristi yana sulhunta duniya zuwa kansa, ba ya lisafta laifuffukansu a gare su ke nan, ya kuma damka mana maganar sulhu. Mu fa manzanni ne a madadin Kiristi, sai ka ce Allah yana yin roko ta wurinmu, muna rokonku madadin Kiristi, ku sulhuntu ga Allah. Shi wanda ba ya son kowane zunubi, ya maishe shi ya zama zunubi saboda mu; domin mu zama adalcin Allah a cikinsa.”
Ina so ne in karfafa cewa, idan ka dauki adalcin mutum ka kwatanta shi da adalcin Allah, ba su ma da kamanni ko kadan. Littafi Mai tsarki ya kwatanta shi da tsumma mara amfani. Godiya ta tabbata ga Allah domin samun ceto ba sai da kudi ko kuwa wani aikin kirki ba, kyauta ce ta wurin alherinsa kawai. Afisawa 2:4-9 tana cewa: “Amma Allah, domin mawadaci ne cikin jinkai, saboda kaunarsa mai yawa wadda ya kaunace mu da ita, ko lokacin da muke matattu cikin laifuffukanmu, ya rayar da mu tare da Kiristi (ta wurin alheri ne an cece ku), ya tashe mu tare da shi, ya zaune mu tare da shi cikin sammai, cikin Kiristi Yesu: domin cikin zamunna masu zuwa ya bayyana mafificiyar wadatar alherinsa cikin nasiha zuwa gare mu cikin Kiristi Yesu. Gama bisa ga alheri an cece ku ta wurin ban-gaskiya, wannan kuwa ba daga gare ku ba ne, kyauta ce ta Allah: ba daga ayyuka ba ne, kada kowane mutum ya yi fahariya.”
Samun ceto shi ne abu na farko idan har muna so mu zama masu adalci bisa ga sharadin Ubangiji Allah. Samu ceton nan ne zai sa mu zama masu adalci, ba domin kyawawan ayyuka da muka yi ba, amma domin karbar shirin da Allah ya yi ta wajen mutuwar Yesu Kiristi a bisa gicciye a matsayin hadaya mai tsarki domin fansar dukan duniya; maganar Allah ta ce: “Gama Allah ya yi kaunar duniya, har ya ba da dansa, haifaffe shi kadai, domin duk wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya samu rai na har abada: (Yohanna 3 : 16). da yake Yesu Kiristi mai adalci ne idan har muna cikinsa, za mu zama masu adalci kamarsa, haka kuma rayuwarmu za ta gamshi Ubangiji Allah; ba domin wani abu da muka yi ba sai dai ta wurin alherinsa kawai, shi ya sa babu mai fahariya.
Matakina biyu kuwa; bayan mun samu ceto ta wurin ban-gaskiya cikin shirin alherin Allah zuwa gare mu, sai: Zama bayin adalci: a cikin Littafin Romawa 6:12-22: maganar Allah tana koya mana cewa: “Kada zunubi fa ya yi mulki cikin jikinku mai mutuwa, da za ku biye wa sha’awoyinsa; kuma kada ku ba da gababuwanku ga zunubi alatun aikin rashin adalci, amma ku mika kanku ga Allah, wato masu rai daga cikin matattu, gababuwanku kuma alatun adalci zuwa ga Allah. Gama zunubi ba zai samu mulki bisa kanku ba, gama ba karkashin shari’a kuke ba, amma karkashin alheri. Me ke nan? Mu yi zunubi domin ba mu karkashin shari’a ba, amma karkashin alheri? dadai! ba ku sani ba, shi wanda kuke mika kanku bayi gare shi garin biyayya, nasa bayi kuke wanda kuke biyayya da shi; ko na zunubi zuwa mutuwa, ko kuwa na biyayya zuwa adalci? Amma godiya ga Allah, koda yake ku bayi ne na zunubi a da, da zuciya daya kuka zama masu biyayya ga wannan irin koyarwa inda aka kai ku; da aka ’yantar da ku daga zunubi kuma, kuka zama bayin adalci. Ina magana irin ta mutum, saboda raunin jikinku; gama kamar yadda kuka ba da gababuwanku bayi ga kazanta da mugunta kuma zuwa mugunta, haka nan kuma yanzu sai kuka ba da gababuwanku bayi ga adalci zuwa tsarkakewa. Gama sa’ar da kuke bayin zunubi, yayayyu ne ku ga zancen adalci. Wane amfani kuke da shi a loton nan cikin al’amuran da kuke ganinsu abin kunya ne yanzu? Gama matukar wadannan al’amura mutuwa ne. Amma yanzu ’yantattu daga zunubi, har kun koma bayi ga Allah, kuna da amfaninku zuwa tsarkakewa, matuka kuma rai na har abada.”
Gababuwan jikinmu kayan aiki ne, za mu iya mika su ga Allah domin ya yi aikin adalci, ko kuwa za ka iya mika shi ga Shaidan domin ya yi aikin kazanta da mugunta da shi, zabi ya danganta da irin rayuwarka a yanzu, za ka iya sanin wanda kake bauta wa ta wurin duba irin halayenka na yanzu, ka san irn abubuwan da kake yi, wane ne kake bauta wa? Za ka iya zama da addini, amma addini ba adalci ba ne ko kadan,tushen adalci shi ne ban-gaskiya cikin Yesu Kiristi a matsayin mai ceto.
Za mu ci gaba daga wannan wuri a mako na gaba idan Allah ya bar mu a cikin masu rai. sai mu ci gaba da yin addu’a domin wannan kasa tamu, domin Ubangiji Allah ya ba mu zaman lafiya da kuma kaunar juna. Allah ya taimake mu. Amin