✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IIimin Firamare: Boko ko bokoko?

A watan da ya gabata ne na ci karo da wani bayani mai ban-haushi, duk kuwa da cewa na dade da sanin bayanin. A zatona zuwa…

A watan da ya gabata ne na ci karo da wani bayani mai ban-haushi, duk kuwa da cewa na dade da sanin bayanin.

A zatona zuwa yanzu abin ya canja, an samu ci gaba fiye da shekarun baya. Amma kasancewar Hukumar Kula da Ilmin Firamare ta Kasa, (UBEC) ce da kanta ta bayyana cewa kashi 71 bisa 100 na yaran da ke gararamba a kan titi ba su zuwa makaranta, duk a Arewa suke, abin ya tayar mini da hankali sosai.

Ganin haka, sai na shiga tunani da bincike ko zan iya samun akasin haka. Ina da makwabcin da ke koyarwa a makarantar firamare ta gwamnati. Ranar Juma’ar da ta gabata, sai na tunkare shi da waccan kididdiga da UBEC ta yi mai nuna yawan yaran da ba su zuwa makaranta a Arewa. Maimakon malamin ya yi mamaki ko bata rai, sai ya yi dariya sannan ya ce mini, “Wannan ai ba tashin hankali ba ne. Tashin hankalin ai sai ka shiga makarantun firamare na gwamnati. Wadanda ake cewa suna karatun su ne ma masu matsala, ba wadanda ba su zuwa makarantar ba.”

Ya ci gaba da ba ni labarin matsalolin da kuma yadda ilimin firamare a makarantaun gwamnati ya lalace kwata-kwata, duk kuwa da biliyoyin Naira da Gwamantin Tarayya da gwanatocin jihohi ke ware wa ilimin. Tambaya a nan, ita ce anya ana kashe kudaden a fannin ilimin kuwa, ko dai kashe-mu-raba ake yi da su?

“Ka ga dai farkon fara koyarwata a wannan makaranta a cikin wannan shekara, dukan ’yan aji hudu sai da na koya musu yadda za su rubuta sunansu da sunan iyayensu. Sannan daga aji daya har zuwa aji shida za ka samu yaro sama da 100. To don Allah yaya za a yi ka iya koya musu har su gane? Abin takaici kuma a kasa suke zama suna daukar darasi,” Malamin ya shaida mini.

Kamar yadda ’yan firamare na gwamnati suke a Kano, haka suke a Katsina, haka a Sakkwato haka a Kebbi, ballantana Yobe ko Bauchi.

A da rajistar da ke dauke da sunayen daliban kowane aji, ba su wuce 40 ba. Amma a yanzu rajistar dalibai a Jihar Kano tana dauke da sunayen dalibai 160, wato shafi daya dauke da sunayen maza 80 ko sama da haka, wani shafi kuma dauke da sunayen mata 80 ko kasa da haka, kuma duk a aji daya.

Malamin nan ya kara da cewa a yanzu saboda yawan yara a aji, ba a ma cika kiran sunaye da safe ba. Ke nan malami bai ma san wanda bai zo ba ko wanda bai zuwa dungurungum.

Idan mutum yana ji ko ganin irin wannan abin takaici, sai ya yi tunanin shin ina Ministan Ilimi? Anya yana sane da wannan babbar matsala? Daga lokacin da ya hau mukamin Minista, shin ya taba shiga wani ajin firamare na gwamanti a Karamar Hukumar Kura ta Jihar Kano ko karamar hukumar da aka haife shi a Jihar Bauchi?

Shin kwamishinonin ilimi kan kai ziyara makarantun nan ko kuwa sai dai kasafta kudin ilimi kowane wata?

A lokacin da na yi karatun firamare, komai kyauta ake bayarwa a makaranta. Biro ko fensir kawai yaro zai rika saye. Amma hatta littattafan karatu da na rubutu duk kyauta ake bayarwa a makaranta. Amma yanzu komai sai iyayen yaro sun saya masa, kuma a makarantar gwamnati wadda a wancan lokacin kudin da jihohi ke samu ba su  kai farashin bajimin sa daya tal a yanzu ba. Amma duk da haka ilimin a kyauta aka rika ba mu shi. A yanzu kuwa da ana koyon abin kirki ma, to da dan dama-dama, amma duk inda ka ji wani dalibi ya yi bajinta, ba za ka taba jin ya fito daga makarantar gwamnati ba, sai dai makarantu masu zaman kansu.

Kiri-kiri wadansu gwamnoni a Arewa suka yi alkawari idan suka ci zabe, to za su cire ’ya’yansu daga makarantun kudi su mai da su makarantun gwamnati don su yi karatu tare da ’ya’yan talakawa. Duk sun ci zaben amma shiru kake ji kamar an shuka dusa, kuma an sa musu ido.

Idan mai karatu zai tsaya ya yi nazari, zai fahimci kawai dai dan talaka ne aka bari a makarantun firamare na gwamnati. Makarantun sun kusa komawa zaurukan hira da cibiyoyin tatsuniya da wasannin harbat-ta-mati kawai. Daga inda aka ce ’yan aji hudu ba mai iya rubuta sunansa da na mahaifinsa, to me ya rage kuma?  Sai mu tambayi kwamishinoni, shin boko yara ke zuwa koyo ko dai bokoko?

Kun ga ashe gwamnati ce ke kyankyashe yaran da ba su zuwa makaranta da kanta. Shi yaya sa za ku ga iyayen yara a kauye suna hana ’ya’yansu zuwa sakandare ko da kuwa gwamnati ta dauke su ba tare da sun ci jarrabawa ba. To me danka zai je ya koya a sakandare har tsawon shekara shida, bayan ya shafe shekara shida a firamare bai iya rubuta sunansa da naka sunan ba?

Yawanci dalili ke nan a birane talakawa ke dora wa ’ya’yansu talla suna bin lunguna da kasuwanni suna tallar awara ko nakiya da alkaki, saboda sun kammala firamare ba su iya rubuta sunansu ballantana sunan iyayensu. Shi kuma Minista ba abin da ya shafe shi, domin babu ’ya’yansa a makarantun firamare. Ina ruwan kwamishina ko gwamna, kai dai a bar su wajen ba da labarin kwangilolin gina ajujuwa ko yi wa ajujuwa kwaskwarima. Da an buda baki sai a ce an kashe biliyan kaza. Amma idan aka ce wa dan firamare “How old are you?” sai ya ji kamar Zabarmanci kake yi masa, ba Inigilishi ba.

Da yawan malaman firamare a yanzu ba su wuce su zauna ajin firamare a koyar da su ba, wanda ya yi gardama to ya jarraba shida daga cikin goma ya sha mamaki. Kowa babu abin da ke zuciyarsa sai iya lissafin saura kwana kadan wata ya kare a yi albashi kawai.

Da yawan malaman firamare a yanzu acaba suke yi ko tuka baburan A Daidaita Sahu. Wadansu ma jigilar kaji suke yi suna bin kasuwannun kauyuka a ranakun karatu. To kai yaya ka gani? Tunda Minista ko Kwamishina bai damu da lalacewar karatun firamare ba, malami na ganin ai shi ma ba sai ya takarkare ya tilasta wa yaro sai ya iya rubuta sunansa ba. Tunda za a bayar da kwangiloli malamai su karbi albashi, wa zai koma ta kan karatun ’yan firamare, ’ya’yan talakawa masu karatun bokoko?

Auwalu Nakarkata Dambatta 08140303173