dan kwallon kulob din Watford na Ingila kuma haifaffen Najeriya Odion Igahlo ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon Afirka da ke buga kwallo a gasar rukunin firimiya ta Ingila.
Gasar wacce ake gudanar da ita a tsakanin ’yan kwallon da suka fito daga Nahiyar Afirka amma suke wasa a gasar rukunin firimiya, ana yin ta ne a duk karshen wata. Wata cibiya da ke kula da yadda ake tafiyar da harkokin kwallon kafa mai suna New African Soccer ce take gudanar da gasar.
A wata sanarwa da cibiyar ta fitar wacce ta samu sanya hannu Daraktanta Tunde Adelakan ta ce “ Abin da ya sa aka zabi Ighalo ba tare da hamayya ba shi ne ganin yadda ya shafe daukacin watan Disamban 2015 yana zura kwallo a wasanni shida da ya buga wa kulob din Watford a gasar firimiya. Hasalima dan kwallon ya samu nasarar zura kwallaye a ragar Chlesea da Liberpool da Tottenham a wasannin firimiyar da ya gudana a Ingila a watan Disambar 2015. Hakan ce ta sa aka zabi dan kwallon a matsayin Gwarzon dan kwallon firimiya na watan Disamban 2015 ba tare da hamayya ba”.
Tunde Adelakan ya ce a tsawon lokacin da aka yi ana gudanar da wannan gasa, Ighalo ne ya kasance na farko da ya lashe kyautar har sau biyu. Ya taba lashe gasar a watan Oktoban 2015 kafin yanzu da ya sake lashe wa a watan Disamban 2015.
Ighalo dai ya zura kwallaye 14 daga cikin wasanni 20 da ya yi wa kulob din Watford a gasar firimiya. Kawo yanzu shi ne dan kwallo na uku a jerin sunayen ’yan kwallon da suka fi zura kwallo a raga a gasar.
Ighalo ya lashe gwarzon dan kwallon Afirka na Ingila
dan kwallon kulob din Watford na Ingila kuma haifaffen Najeriya Odion Igahlo ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon Afirka da ke buga kwallo…