An bai wa hamata iska tsakanin ’yan acaba da ’yan sanda kan dokar hana sana’ar acaba a yankin Idi-Araba da ke Jihar Legas.
A ranar Talata ne dai ’yan acaba suka yi bore a Idi-Araba kan kwace musu babura da jami’an kwamitin aiki da cikawa da Gwamnatin Jihar ta kafa kan dokar hana sana’ar tasu.
Bidiyon yadda lamarin ya faru da aka yada a kafafen sada zumunta sun nuna ana kone-konen tayoyi a kan tituna, wasu mutane da ake zargin ’yan acaba ne kuma suna guje-guje a kan titi, a yayin da masu shaguna suke ta rufewa saboda tsoron abin da zai iya biyowa baya.
Kafar PremiumTime ta ruwaito wani jami’in Asibitin Koyarwa dan Jami’ar Jihar Legas da ke Idi Araba na cewa dauki-ba-dadin da bangarorin biyu suka yi da misalin karfe 11 na safiyar Talata ya sa an rufe babbar kofar shiga harabar asibitin.
Zanga-zangar ’yan acabar ta kawo tsaiko ga gudanar da harkoki da zirga-zirga a yankin na Idi-Araba tun da safiyar ta Talata.
Zanga-zangar tasu na zuwa ne kimanin mako biyu bayan wani dauki-ba-dadi da aka tsakanin ’yan sanda da ’yan acaba a yankin Ojo na jihar, bayan ’yan sanda sun yi yunkurin hana gudanar da sana’ar a yankin.
A makon jiya ne dai Gwamnatin Jihar Legas ta markade babura 2,000 da ta kwace daga hannun ’yan acaba da suka karya dokar haramcin da ta sanya wa sana’ar.
A ranar 1 ga watan Yuni, 2022 da muke ciki ne dai gwamnatin jihar ta sanar da haramta gudanar da sana’ar a kananan hukumomin Apapa da Eti Osa da Ikeja daLegas Island, Lagas Mainland da kuma Surulere.
Amma daga baya, kakakin ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce ’yan sanda daga rundunar RRS sun tarwatsa ’yan acabar kuma sun dawo da doka da oda a yankin.
Ya ce, “Wasu ’yan acaba marasa bin doka sun nemi tayar da fitina bayan an kwace baburansu, amma mun girke jami’anmu, kuma Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, Abiodun Alabi, da kansa ne ya jagoranci aikin.”