Wani matashi mai suna Nura Maidabino da yake sayar da dabino ya ce, ko aikin gadin makarantar garinsu a Jihar Jigawa karamar hukumarsu ta dauke shi zai bar tallar dabino da yake yi.
Matashin ya yi zargin cewa wadanda aka dauka aikin suna yin watsi da shi su kama gabansu.
- APC ta lashe dukkan kujerun Ciyamomi da Kansiloli a zaben Filato
- Marwa ya yi gargadi kan halasta tabar wiwi a Najeriya
Nura wanda ya zanta da Aminiya a garin Kalaba ya ce, da farko fataucin sayar da awaki ne ya kai shi Kurmi kafin daga bisani ya rikide ya koma sayar da dabino.
“Na samu shekara 10 ina sayar da dabino a nan garin Kalaba babban birnin Jihar Kuros Riba. Amma fataucin kawo awaki ya sa na koma sayar da dabino kuma Alhamdulillah ina samun nasara tunda na kama kasuwancin,” inji shi.
Ya ce, “Farko na fara sayen dabino kwano takwas daga Kano in zo da shi, ban san ana sayarwa a Kwanar Babaldu ba, daga baya na rika saya a Kwanar Babaldu.”
Nura Ubale ya bayyana nasarorin da ya ce ya samu tun daga lokacin da ya fara sayar da dabino tsawon shekara 10 Kalaba.
“Na mallaki muhalli na kaina ina da aure sai burin kara wata matar, babu abin da zan ce wa kasuwanci sai godiya ga Allah,” inji shi.
Ya yi kira ga matasa da sauran jama’a da ba su son yin sana’a ko kasuwanci sai yawo a gari, da cewa, sana’a ta fi zaman banza ko yawon bambadanci da mutane suke kashe zuciyarsu suna yi.
Sai ya yi addu’ar Allah Ya kawo wa kasar nan karshen fitinun da suke faruwa a kowane sashe na kasar nan.