✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Idan na fadi zaben 2023 zan rungumi kaddara —Kwankwaso

Kwankwaso ya ce matukar aka gudanar da sahihin zabe, zai aminta da sakamakon da aka samu.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce zai amince da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 idan har bai samu nasarar lashe shi ba.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne ranar Litinin a wani taro da ya yi da ma’aikata da daliban Jami’ar Abuja.

Sai dai ya ce akwai bukatar a gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya kuma ce, “Ba ni da matsala da amincewa da faduwa zabe. Hanya mafi kyau ta yarda da zaben 2023, ita ce ta hanyar yin abin da ya dace – wato yin zabe na gaskiya, zaben da kowa zai aminta da shi,” in ji shi.

Kwankwaso, wanda kuma tsohon Ministan Tsaro ne, ya yi alkawarin kara wa sojojin kasar nan karfi, a wani yunkuri na sabunta dabarun tsaro.

A yayin taron Kwankwaso, ya jaddada wa dalibai da ma’aikatan Jami’ar kudurinsa na farfado da harkar ilimi a kasar nan, inda ya bayyana irin tanadin da ya yi wa harkar.

“Mun yanke shawara kuma muna nan kan tsarinmu cewa za mu magance matsalar rashin tsaro.

“Za mu ba da dama mai yawa ga matasa maza da mata su yi wa kasar nan hidima a matsayin jami’an soja, ’yan sanda, jami’an DSS da sauransu.”

Game da batun yiwuwar janye wa wani takararsa kuwa, Kwankwaso ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe.