✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan muka samu tallafi za mu iya kera komai – Alhaji Isma’il

Alhaji Isma’il Ahmad wani mai sana’ar hannu ne a Kasuwar Panteka (Tsohuwa) da ke Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana yadda ya fara sana’ar…

Alhaji Isma’il Ahmad wani mai sana’ar hannu ne a Kasuwar Panteka (Tsohuwa) da ke Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana yadda ya fara sana’ar da kuma dabarun da yake bi wajen kere-keren kayayyakin biyan bukatun yau da kullum da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?
Alhaji Isma’il:  Suna na Alhaji Isma’il Ahmad, amma an fi sanina da sunan Green White Green. Da ina aikin  tinka ne wato aikin holoko, sannan na koyi waldan kofan da harshashi baya hudawa, na kuma kara gaba inda na fara kere-kere, wato idan na ga abu sai in kera kamarsa a fanteka har na ware na koma layin Enugu Road da ke Tudun Nupawa Kaduna.
Aminiya: Ya kake samun sinadarin hada kayayyakin aiki?
Alhaji Isma’il: Ana tsinto holoko ne, sai a kawo a auna a saya sannan a sarrafa su a yi kwanuka da dai sauransu.  
Aminiya: Yaushe ka fara wannan sana’ar?
Alhaji Isma’il: Na fara ne wani lokaci da mutane suka fara kawo kaya da suka karye, ko suka lalace suna cewa suna so a gyara musu da kuma wanda suke so a kera musu. Abubawan da nafara kerawa ana yi mini dariya sun hada da Faifan kwanon setilat, rishon wutan lantarki wanda har kasar Nijar ake kaisu a sayar da yawa don kasar tana da wutan lantarki fiye da Najeriya, da na’uran yin kankara da abubuwa da dama wanda manyan otel da gidajen sayer da abinci ke bukata a kullum da masu kifi, yogut da dai sauransu.
Aminiya: Shekaru nawa da ka fara sana’a a wannan kasuwa ta Panteka?
Alhaji Isma’il: Na kai shekara 19 ina hada-hada a wannan kasuwa.  
Aminiya: Ta ya kake gudanar da aikinka?
Alhaji Isma’il: Idan an kawo abu da ya lalace, ko wani abu da ake so a kera kamar shi, sai in kwance wanda aka kawo mini ko wanda ya lalace, ko wanda ake son in kera don ganin yadda cikin sa yake.
Ina daukar mizanin yadda na asalin yake, irin karfen da aka yi da shi, ko noti, ko waya da dai sauransu, sai in nemo kayan in hada, in an gama sai in hada abin muga ko zai yi aiki yadda na asali yake. Wani abin da muke hadawa ya kan fi na baturen karko, kamar na’uran yin kankara da risho da faifen kamo tashoshi mai hoto na kasashen waje.
Aminiya: Ya kake idan wanda yake son kayanka yana zaune nesa da garin Kaduna?
Alhaji Isma’il: An kai wannan na’urar yin kankaran dukkan fadin kasar nan. Sannan akwai lambar waya na an lika a jikin na’urar.
Aminiya: Ya kuke samun kayan aiki?
Alhaji Isma’il: Muna samun su ne daga kayan kotono wato da aka yi amfani da su aka gama daga kasashen waje ko  kuma na tsohon na’uran sanyaya daki wato (AC), sai mu mayar da ita ta yin kankara. Mutane da yawa suna mamakin wannan dabara tamu.
Aminiya: Wane lokaci ne aka fi sayen kayan?
Alhaji Isma’il: An fi sayen kayan ne lokacin da aka fara zafi don bukatan kankara da dai sauransu, amma risho a kullu yaumin ana sayen shi. Shi kuma faifen setilat kasuwarsa ta yi kasa kadan don fitowar kananan faya-faye. Amma fa mai sayen na’uran kankara ya danganta ne da girman bukata da karfin jarin mutum. Akwai kanana da matsakaita da manya. Akwai mai na’urar sanyaya daki guda daya, da mai biyu da babba mai guda uku.
Aminiya: Ko kana da ma’aikata masu taimaka maka?
Alhaji Isma’il: Ina da ma’aikata akalla guda 10, a bangarori uku na yin na’urar kankara, da na kere-kere da na fenti. Amma in aiki ya yi yawa, ko wane bangare na tallafa wa wani bangaren don haka ya sa yarana suna yin aiki a kowane bangare.
Aminiya: Ko masu ilimin kimiyya na boko sun taba tuntubarka?
Alhaji Isma’il: Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Kaduna (Kaduna Polytechnic) wacce tana nan kusa da inda na ke aiki sun taba ziyarta da burin za su rinka kawo dalibai masu sanin makaman aiki (wato ’yan ITF) shekaru bakwai da suka wuce, amma shiru kake ji kamar an shuka dusa.
Aminiya: Shin ko hukumar koya wa matasa sana’o’i wato NDE sun taba tuntubar ka?
Alhaji Isma’il: Ina dai jin sunansu a kafafen yada labarai. Sai dai akwai daliban makarantun Kimiyya da Fasaha da suke zuwa da kansu su koyi aiki kyauta.
Aminiya: Ko kana fuskantar wani kalubale?
Alhaji Isma’il: Da farko dai gwamnati ba ta son sayen kayan da aka kera a nan cikin gida don ba a yi musu gida da fenti sumul kamar na kasashen waje, da rashin wutan lantarki ko da yaushe, da kuma masu karbar haraji ba gyara ba sabar. Najeriya za ta ci gaba ne kawai idan an samar da wutar lantarki ba dare, ba rana.