✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Idan Jonathan na son takara za mu ba shi —APC

Jonathan dai bai ce uffan ba game da tayin da APC ta yi masa.

Jam’iyyar APC mai mulki ta yi wa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan tayin tikitin takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Babban Sakataren Riko na jam’iyyar APC, John Akpanudoedehe, ya ce jam’iyyar za ta iya ba wa Jonathan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 idan ya dawo cikinta ya kuma nuna sha’awarsa ta fitowa takarar.

Mista Akpanudoe ya bayyana hakan ne a cikin shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis.

Ya yi karin bayanin cewa hakan ba yana nufin za su ba Jonathan takara kai tsaye ba ne, sai dai za su ba shi damar tsayawa domin karawa da sauran ’yan takara da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa a 2023.

Sai dai har yanzu tsohon shugaban kasar bai ce uffan ba game da tayin da ake masa na sauya sheka zuwa APC mai mulki.

An dai dade ana rade-radin cewa shugabancin jam’iyyar APC karkashin Mai Mala Buni, na zawarcin Jonathan ya koma jam’iyyar, wanda hakan ya ta da kura a jam’iyyarsa ta PDP.

Duba da yadda zaben 2023 ke ci gaba da karatowa, wasu na ganin cewa Jonathan na iya sauya sheka zuwa APC, sakamakon yadda PDP ke cike da masu neman takarar kujerar shugaban kasa a cikinta.