✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Idan Atiku ya yi wasa zai sha kasa a Zaben 2023 —Wike

Amma idan abin da suke so ke nan, ina yi musu fatan alheri.

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, ya gargadi dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya yi hattara da ’yan kanzaginsa ko ya sha kasa a zaben badi.

Wike ya ce muddin Atiku bai yai taka tsan-tsan ba, to za a wayi gari damar shugabancin kasar nan za ta subuce masa a sakamakon yadda wadanda ke kawaye shi ke dagula masa al’amura.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Juma’ar nan, yayin da Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya kaddamar da rukunin gidajen ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas a birnin Fatakwal.

Wike ya ce akwai wasu ’yan kanzagin Atiku da suka shagaltu da takalarsa a daidai lokacin da ya kamata a ce sun dage kan yadda PDP za ta lashe Zaben 2023.

“Tsara manufofi da dabarun cin zabe shi ne abin da ya kamata ya zama duk masoyan PDP na gaskiya ke yi a yanzu.

“Ya kamata mahangar masoyan PDP a yanzu ta zama yadda za mu lashe zaben badi.

“Amma a yanzu duk wadanda ke neman gindin zama da ke kewaye da shi [Atiku] babu wani alheri da suke suka masa, don kuwa kokarin da suke yi shi ne kada ya ci zabe.

“Amma idan abin da suke so ke nan, ina yi musu fatan alheri.”

A bayan nan ne Wike ya musanta rade-radin kai Atiku da Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal kara kotu kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.