Hukumar Gudanarwar Kungiyar Kwallan Kafa ta Kano Pillars ta dawo da Ibrahim Musa a matsayin mai horar da ’yan wasan kungiyar zuwa karshen kakar wasanni ta bana.
Ibrahim Musa ya karbi aiki ne daga takwaransa Kabiru Baleriya wanda ya jagoranci kungiyar a matsayin rikon kwarya.
Kakakin Kungiyar ta Kano Pillars Lirwanu Idris Malikawa ya bayyana cewa an dawo da koci Ibrahim Musa ne bayan Hukumar Gudanarwar Kungiyar ta yi wani taro a makon jiya inda ta ga dacewar a kara ba shi dama.
A jawabinsa Ibrahim Musa ya yi godiya ga gwamnatin Kano bisa wannan dama da ta sake ba shi.
Ya kuma nemi hadin kan ’yan wasn da dukan ma’aikatan kungiyar da su ba shi hadin kai don kai kungiyar ga gaci.
“Muna so a kara ninka hadin kan da ake ba mu. Mu ’yan Kano ne ko ba mu cikin kungiyar nan ba za mu so mu ga wani abu mara kyau ya samu kulob din ba. Kano din muke kallo da kulob din, don haka a shirye muke mu rungumi kowa yadda za mu yi aiki tare wajen cicciba kulob din gaba yadda za mu kai ga nasara,” inji shi.
Sabon kocin ya kuma nemi afuwar al’ummar jihar bisa kurakuren da ya aikata a baya tare da daukar alwashi kawo canji nagari cikin harkar tafiyar da kungiyar.