Daga Hudubar Sheikh Abu Ibrahim Sa’ud bin Ibrahim as-Shuraim
Masallacin Haramin Ka’aba da ke Makka
Godiya ta tabbata ga Allah Makagin halitta da ake komawa gare Shi. Mai aikata abin da Ya yi nufi, Ya saukar da Alkur’ani Mai girma a cikinsa akwai gargadi da jan kunne da kwadaitarwa da tsoratarwa. “karya ba ta zuwa ta gaba gare shi ko ta bayansa, abin saukarwa ne daga Mai hikima Abin godewa.” Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, shaidar da nake fatar tsira da ita daga narkon azaba. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, mai bushara ga mai neman shiriya, mai gargadi ga mai ketare iyaka, ya nuna duk wani al’amari mai kyau. Ya Allah Ka kara tsira da aminci a gare shi da alayensa tsarkaka da sahabbansa taurarin shiriya da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, wasiyyar da nake gabatar muku ya ku bayin Allah, ita ce ta ku bi Allah da takawa da lizimtar jama’a da tsarkake zuciya da kwance kanku daga sarkakiyar kiyayya da take gadar da kaskanci ta tayar da fitina ta kuma rusa soyayyar da ke tsakanin Musulmi. Ina yi muku hani daga sabani da rarraba domin suna hallaka al’umma, suna cinye kyawawan halaye kamar yadda wuta take cinye kirare. “Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukuncinsa (ku mayar da shi) zuwa ga Allah, wancan Shi ne Allah Ubangijina a gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al’amarina.” (k: 42: 10)
Ya ku mutane! Lallai husuma a tsakanin mutane al’amari ne da ba makawa za ta rika aukuwa, face wadanda Ubangiji Ya yi musu rahama. Domin mafi yawan masu hulda sashinsu na cutar da sashi face wadanda suka yi imani suka aikata ayyuka na kwarai kuma ’yan kadan ne ke hakan.
Ya ku mutane! Asalin abin da ke ga mutane shi ne, rashin sabani da husuma, amma sai hakan ya kau daga lokacin da daya daga cikin ’ya’yan Annabi Adam (AS) ya kashe dan uwansa, sai al’amari ya sauya aka wayi gari sabani da husuma abu ne da ba za a iya kauce musu ba. Sai dai kuma kusancin mutane ga aiki da shari’a, ya rika hana aukuwar hakan daga lokaci zuwa lokaci.
Kuma husuma da makiya ta fi tsanani daga wadda ake yi tsakanin masoya, sannan ta fi aukuwa a tsakanin wadanda suke kusa daga wadanda suke nesa. Kuma ta fi muni a tsakanin makwabta daga tsakanin iyali guda, sannan a cikin ’ya’ya ta fi muni a tsakanin shakikai. Haka dai lamarin yake a tsakanin makusanta da makusanta har zuwa abin da ya sauwaka.
Saboda haka ne shari’ar Musulunci ta zo tana mai sukar husuma, tana yaki da jayayya, tana tsoratarwa kan wuce iyaka a cikinsu da wuce gona da iri a kansu, wato a yi su don neman gano gaskiya, kuma ta sanya wanda yake wuce iyaka ya zamo yana da siffa daga cikin siffofin munafunci, ta hanyar aikata fajirci a lokacin husuma, wato kaucewa daga gaskiya.
Abu ne sananne cewa husuma tana aukuwa a tsakanin mutane kodai a cikin ibadoji ko mu’amaloli, kuma mu’amalar ko ta zamo niyya ce ko magana ko aiki. To duk wanda ya ketare iyaka wajen husuma a wadannan abubuwa uku, yana da yanki na munafunci gwargwadon abin da ya siffantu da shi. Annabi (SAW) ya tara hakan cikin fadinsa: “Alamun munafuki uku ne: Idan ya yi magana ya yi karya; idan ya yi alkawari ya saba; idan aka ba shi amana ya yi ha’inci.” Buhari da Muslim suka ruwaito. A wata ruwayar da ta fi dacewa da batunmu, ya ce, “Idan ya yi husuma ya yi fajirci.”
Fajirci a cikin husuma sulusin mu’amaloli ne, domin magana tana fuskantar kalubale daga karya da fajirci a cikin husuma. Niyya kuma tana fuskantar kalubale daga saba alkawari, yayin da aiki ke fuskantar kalubale daga ha’inci.
Ya bayin Allah! Mai fajirci a cikin husuma shi ne wanda yake sane cewa ba ya kan gaskiya, amma ya tsaya yana kare karyar, har ya auka cikin abin da Allah Ya hana cikin fadinSa: “Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da karya, kuma ku sadar da ita ga mahukunta domin ku ci wani yanki daga dukiyoyin mutane da zunubi alhali kuwa ku, kuna sani.” (k: 2: 188). Wani magabacin kwarai ya ce: “Wannan aya tana magana ne kan mutumin da yake husuma ba tare da hujja ba, kuma ya san ga inda gaskiya take, amma ya kauce mata.”
Ya bayin Allah! Mai fajirci cikin husuma- harshensa yana gaba da hankalinsa, kausasawarsa ita ce hakurinsa, zaluncinsa shi ne adalcinsa, harshensa ba ya da linzami, zuciyarsa kazantacciya ce, yana jin dadin tuhumar wadansu da kauce wa abin da shari’a ta ajiye.
Fajiri a wajen husuma yakan kara karya 100 a kan gaskiya daya. Shi kamar kuda yake, ba ya sauka sai a kan kazantar mutane, yana dubi ne da idon adawa, domin da idon yarda yake dubi da ya kyautata abin da ya baci, ba ya ganin abin kirkin mutane sai zunubansu. Wayyo Allah! Wane uzuri ne mai wannan hali zai bayar? Za ka gan shi yana cin mutuncin mutane, mai zunde mai watsa annamimanci, dan ta’adda mai yawan zunubi. Yana da dabi’a irin ta tsutsa, wadda ba ta shiga cikin abu, face ta lalata shi ko ta kazantar da shi.
Mai fajirci wajen husuma ya bayin Allah! Ba ya da amana kuma ba ya da sutura, yana da dabi’ar zargi. Idan ka saba masa a cikin kankanen abu, sai ya watsa sirrinka ya keta mutuncinka, ya tuno laifinka na baya da na yanzu. Aboki nawa ne ya tona asirin abokinsa, saboda sabanin da bai kai ya kawo ba? Mazaje da yawa sun faffallasa sirrin matansu, saboda gishiri bai ji a miya ba, ko rashin wanke sutura ko makamantan haka.
Ba husuma ne abin zargi ba, tunda abu ne da ba makawa tana cikin zukatan mutane da kwakwalensu da dukiyarsu da mutuncinsu da addininsu, domin babu mutumin da zai iya gamsar da dukkan mutane, abin zargi shi ne ketare iyaka wajen husuma.
Babban abin mamaki ya bayin Allah! Shi ne abu ne mai sauki a wurin mutane da dama su ci haram ko su yi zina ko su yi zalunci da sata da sauransu, amma abu ne mai wahala a gare su, su tsare harshensu. Mutum nawa ne muke gani suna aikata wadannan miyagun ayyuka da alfasha, suna tsoma harsunansu cikin cin mutuncin mutane, ba tare da sun damu da abin da za su fada ga abokan husumansu ba, alhali Allah Madaukaki Yana cewa: “Lallai Allah Yana yin umarni da adalci da kyautatawa, da bai wa ma’abucin zumunta, kuma Yana hani daga alfasha da abin da aka ki da rarrabe jama’a. Yana yi muku gargadi tsammaninku, kuna tunawa.” (k:16:90).