Manjo Janar Zamani Lekwot (mai ritaya) ya soki malaman Musulunci da suka bukaci a zartar da hukuncin kisa da kotu ta yanke masa saboda samunsa da hannu a kashe-kashen da aka yi a rikicin Zangon Kataf a 1992.
Martaninsa ke nan ga Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya da ta yi kira da cewa in har ana son zaman lafiya ya wanzu a Kudancin Kaduna to sai an zarta da hukuncin kisa da kotu ta yanke wa Lekwot da sauran mutane goma sha shidda (16).
A jawabin da Lekwot ya yi, ya ce, “Abin da Najeriya take bukata a wannan lokacin shi ne hakuri da juna, a manta da kabilanci ko bambancin addini ko tsanar juna.
“Rayuwata ba a hannun malaman Musulunci take ba, a hannun Allah take. Babu wani abu da zan ce”, inji Lekwot
Da yake magana da ‘yan jarida jim kadan bayan taron nuna rashin jin dadi da Kungiyar Kiristoci (CAN) ta yi a ranar Lahadi, Lekwot ya kara da cewar, shugannin addini na kwarai kamata ya yi su yi kira da a so juna ba su rika horo da kiyayya da rarrabuwar kai a kasa ba.
“Maganar Zangon Kataf da suke yi; Kwarai kisan abun Allah-wadai ne, amma rikicin ya faru ne saboda sauya wa kasuwa wuri. Wasu mutane ba su so hakan ba, amma daga karshe an nada kwamitin bincike, ya kuma gabatar da shawarwarin da suka kamata.
“An kuma aiwatar da shawarwarin da kwamitin Mu’azu ya bayar. Saboda haka wadanda suke kokarin waiwayarsa suna nuna taurin kai ne. Abin da muke bukata a kasar nan shi ne hakuri da juna; muna tare da juna na lokaci mai tsawo”.
Sai dai ita Majalisar koli ta Sharia a Najeriya, a takardar da ta fitar ta dage cewar idan aka zartar wa su Lekwot da hukuncin kisan zai zama darasi ga duk wanda ke kokarin haddasa fitina a yankin.
Kotu ta musamman da Tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Babangida ya kafa kan rikicin Zangon Kataf a shekarar 1992, karkashi jagorancin Mai Sharia Pius Okadigbo, ta yanke hukunci kisa ta hanyar rataya ga Lekwot da sauran mutanen kan samunsu da hannu tsundum a cikin rikicin.
Daga baya aka sassauta hukuncin zuwa zaman jarun, kafin gwamnatin marigayi Janar Sani Abatcha ta yafe masa a shekarar 1995.
Sakataren Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya, reshen Jihar Kaduna, Injiniya Abdulrahman Hassan, a taron ‘yan jarida da ya gudanar, ya ce yafiyar da aka yi wa su Janar Lekwot ce ta jawo ci gaban rikice-rekicen da ake ta fama da su har yanzu a Kudancin Kaduna.