Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong, ya yi gargadin cewa nan ba da dadewa ba zai sanya hannu a kan dokar zartar da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane a Jihar.
Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a fadar Gwamnatinsa da ke birnin Jos yayin rantsar da sabon Shugaban Kotun Al’adu na jihar da wasu sabbin Alkalai guda biyar na kotun.
- Gwamnatin Kaduna ta sanar da ranar sake bude makarantun sakandiren jihar
- An rushe gidan wadanda ake zargi da satar mutane a Kuros Riba
Gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda ayyukan garkuwa da mutane suka yawaita a jihar, lamarin da ya ce ana kama wadanda ake zargi sannan ake sakinsu ba tare da an hukuntasu ba.
“A matsayina na gwamnan jihar nan, na yi alkawarin zan sanya hannu a rika zartar da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin aikata garkuwa da mutane a jihar nan.
“Zan yi hakan ne ganin yadda wannan al’amari ya jefa al’umma cikin damuwa na biyan makudan kudaden fansar ‘yan uwansu ga wadannan bata gari’’.
Ya yi kira ga sabbin Alkalan da su yi aiki da rantsuwar da suka dauka ta hanyar rike gaskiya da amana wajen gudanar ayyukansu.
Da yake jawabi a madadin sabbin Alkalan, sabon shugaban kotun, Mai Shari’a Sati Patrick Dapit, ya bada tabbacin cewa za su yi iyaka bakin kokarinsu wajen ganin sun rike wannan rantsuwar kama aiki da suka yi.
Sauran sababbin Alkalan da aka rantsar sun hada da Mai shari’a Naankwat Dawat Shaseet da Buetnaan Mandy Dongban Bassi da Pauline Nanlep Njar da Edwin Sati Munlang da kuma Georgina Dashe.