✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukuncin daurin rai-da-rai: Ra’ayoyin ‘yan uwan Musulmai 51 da aka kashe

Mutanen da suka tsira da kuma ‘yan uwan Musulmi 51 da Brento Tarrant ya kashe a kasar New Zealand sun bayyana ra’ayoyinsu kan hukunci daurin…

Mutanen da suka tsira da kuma ‘yan uwan Musulmi 51 da Brento Tarrant ya kashe a kasar New Zealand sun bayyana ra’ayoyinsu kan hukunci daurin da aka yanke masa.

Tarrant mai shekara 29 ya rutsa musulmai a masallatai biyu ranar Juma’a, 15 ga watan Maris, 2019 inda ya harbe mutane hamsin har lahira, tare da raunata 40.

Ya kuma yi amfani da kyamarar goshi wajen daukar bidiyon aika-aikan da ya ke yi tare da yadawa kai tsaye a Facebook.

Abdul Azeez Wahabzadah wanda ya jefi Tarrant da na’urar POS a kai, Wanda hakan yasa mutane da dama suka tsira ya ce hukunci daurin rai-da-ran ya yi daidai.

“Dama wannan hukunci muka ga ya fi dacewa da shi kuma muka samu,” ya kuma ce Tarrant “matsoraci ne” kuma “wawa ne” da ya lalata rayuwarsa.

Ahmed Wali Khan, wanda ya rasa kawunsa a harin Christchurch din aka kai ya ce al’ummar Musulmi sun yi farin ciki da hukuncin.

“Kowa yana murnar ganin an hukunta mai laifin bisa adalci. Mun dade muna jirar wannan hukunci”, inji shi.

Taj Kamran, wanda ya tsira da harbin bindiga da dama a kafarsa, kuma har yanzu sanda yake dogarawa, cewa ya yi, “Hukuncin ba za a maido wadanda suka rasa rayukansu ba, “amma yanzu muna iya yin barci”.

Da yake karanta hukunci, Mai shari’a, Cameron Mander, na Babbar Kotun da ke zama a Christchurch, ya ce abin da Tarrant ya aikata ” Dabbanci ne” da “rashin tausayi”.

“Laifin da ka aikata kazami ne, kuma ko da an tsare ka har bayan rayuwarka, hukunci ba zai yi daidai da abun da ka aikata ba”.

Tarrant bai nuna wata damuwa ba a lokacin da alkalin ya ce zai karasa sauran shekarunsa da suka rage masa a duniya a kurkuku ba tare da lamuni ba.

Wannan shi ne hukunci mafi tsanani da kasar New Zealand ta taba yanke wa wani mutum irinsa a tarihi.

Kasar ta New Zealand ta hana zartar da hukuncin kisa ga wanda ya yi kisa tun shekarar 1961.