✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukuncin daga hannu sama a yi addu’a bayan an gama sallar farilla (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da…

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah, Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni zuwa ga samun alheran duniya da Lahira; (Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsa cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  
Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta, amin.
Bayan haka, mun kwana a wannan mukala bayan gabatar da amsar tambayar da aka yi wa marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam a kan haka, to yau, in Allah Ya so, za mu ga amsar shehunan malamai biyu kamarhaka:
Yayin da ya amsa tambayar mene ne hukuncin daga hannaye da addu’a bayan Sallah, a cikin littafinsa Fatawal Akidah wa Ma’aha Fatawas Siyam wal Hajji waz Zakkah was Salah, Sheikh  Muhammad bn Salihul Usaimin ya ce:
“Ba ya cikin abin da aka shar’anta cewa idan mutum ya kammala Sallah ya daga hannayensa ya yi addu’a. Idan ma har mutum yana nufin yin addu’a ne, to yin ta cikin Sallah shi ne ya fi dacewa a kan kasancewarta bayan ya fita daga cikin Sallar. Kuma da wannan ne Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yi nuni a cikin Hadisin Abdullahi dan Mas’ud (Allah Ya yarda da shi), a yayin da ya ambaci tahiyya, ya ce, “…Sannan, sai (mai Sallah) ya zabi irin addu’ar da ya so (ya yi)…”
“Amma abin da gama-garin mutane (ammah) suka kasance suna aikatawa na zaman duk lokacin da suka yi Sallah ta nafila, sai su daga hannayensu, har ma sai ya kasance, wani sashensu, yakan ce, ‘ban yi addu’a ba’ (wato zai kasance ya rika jin kamar ma dai bai yi komai ba); da yawa ma za ka ga an tayar da Sallar Farilla, alhalin shi yana cikin tahiyyar nafilarsa, har idan ma ya sallame, sai ya daga hannayensa da gaske, kamar dai ka ce – Allah Shi ne Mafi sani – ko daga hannun wani abu ne wanda aka wajabta masa, sannan sai ya shafa fuskarsa. Dukkan wannan aiki, abin kiyayewa ne da lura a kan addu’ar da suke zaton shari’a ce, alhali ba a shar’anta ta ba. Abin da ma ya kamata a lura da shi a kiyaye a nan shi ne wannan yanayi yana iya fuskantuwa zuwa ga bidi’a (abin da aka kirkira).”
Shi kuma Sheikh Abdul’aziz bin Abdullahi bin Baz a amsar da ya bayar kan tambayar da aka yi masa ko mene ne yake gani cikin daga hannaye don yin addu’a bayan kare Sallah, ko a cikin yin haka akwai bambanci tsakanin Sallar Farilla da ta Nafila, (a cikin littafinsa Fatawal Muhimmah Tata’allaku Bis Salah, wanda aka yi wa bugun farko a shekarar 1413 Bayan Hijira, kimanin shekara 24 ke nan), ya ce:
“Shi al’amarin daga hannaye cikin yin addu’a Sunnah ne kuma yana daga cikin sabubban karbuwarta, saboda fadin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), “Lallai Ubangijinku, Mai jin kunya ne, Mai karimci. Yana jin kunyar bawanSa idan ya daga hannayensa zuwa gare Shi, sannan ya komo da su wayam (ba komai – ke nan manuniya cewa ana karba masa).” Abu Dawuda da Tirmiziy da Ibnu Majah suka fitar da Hadisin, kuma Hakim ya inganta shi daga Hadisin Salmanul Farisiy (Allah Ya yarda da shi). Sannan da fadinsa, (Sallallahu Alaihi Wasallam), “Lallai Allah – Ta’ala – Tsarkakakke ne, ba Ya amsa (karba), sai abin da yake mai tsarki.  Kuma lallai Allah Ya umurci muminai da abin da Ya umurci Manzanni, indaYa ce, “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ci daga dadadan abubuwan da Muka azurtaku (da su), kuma ku yi godiya ga Allah, in har kun kasance a gare Shi kadai kuke yin bauta.” Suratul Bakara, aya ta 172. Kuma Allah, Mai girma da daukaka Ya ce, “Ya ku Manzanni! Ku ci daga dadadan abubuwa, kuma ku aikata aiki wanda yake nagari, lallai Ni, Mai gani ne dangane da abin da kuke aikatawa.” Suratul Mu’minun, aya ta 51. Sannan ya ba da labarin wani mutum da yake cikin doguwar tafiya, kansa a hargitse, jikinsa da kura, yana mika hannayensa sama (yana cewa), ya Ubangiji! Ya Ubangiji! (yana rokon Allah bukatunsa) alhali abincinsa na haram ne; abin shansa na haram ne; tufafinsa na haram ne; an ciyar da shi da haramun, ta kaka za a amsa masa?” Muslim ne ya fitar da shi, a Hadisi na 1015.
“Sai dai, yadda al’amari yake, shi ne ba a shar’anta daga hannaye a cikin wuraren da suke an same su a zamanin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), kuma bai daga hannaye a cikinsu ba, kamar bayan kare sallolin farillan nan guda biyar da tsakanin sujadai biyu; da gabanin sallame Sallah da lokacin Hudubar Juma’a ko idoji biyu ba; saboda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam, bai daga hannu a cikin dayan wadannan wurare ba, alhali shi, mai tsira da amincin Allah, shi ne abin koyi mafi kyau na daga abin da ya wuce da abin da zai zo nan gaba. Sai dai idan yana addu’ar rokon ruwa a lokacin Hudubar Juma’a ko ta idoji biyu, to an shar’anta masa daga hannayensa, kamar dai yadda ya aikata, a cikin wadannan halaye.
“Amma a Sallar Nafila, ni ban san wani da ya yi hanin a daga hannaye bayan kammala ta a yi addu’a ba, domin aiki da gamuwar dalilai a kan haka, sai dai abin da ya fi dacewa shi ne kada a doge kan yin haka, wato kowace nafila aka yi a ce sai an daga hannaye an yi addu’a.  Saboda yin haka bai tabbata cewa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya aikata shi ba.  Kuma lallai da dai ya aikata haka din, a bayan kowace nafila, to da an cirato (ruwaito) hakan daga gare shi, saboda su sahabbai (Allah Ya yarda da su), lallai sun cirato zantuttukansa (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ayyukansa a cikin tafiye-tafiyensa da zamansa a gida. Kai, da ma dai dukkan halayensa na rayuwa (Allah Ya kara musu yarda gaba dayansu).
“Hadisin da ya shahara a tsakanin mutane, cewa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Sallah tana sanya tadarru’i (kaskantar da kai) da khushu’i (nuna gazawa ga Wanda ya isa) da kana’a (yarda da abin da aka ba mutum), wato ka daga hannayenka kana cewa, ya Ubangiji! Ya Ubangiji…!” Hadisi ne mai rauni (da’ifi), kamar yadda Alhaafiz Ibnu Rajab da waninsa suka yi gamsasshen bayani kansa.Allah Shi ne Majibincin dacewa.”
Wannan shi ne karshen bayanin malaman. Sannan akwai wata manuniya a littafinTaisiiril Allam, wanda sharhi ne na Umdatul Ahkaam na Sheikh Abdullahi bn Abdurrahman bn Salih Ali Bassam, a shafi na 283, inda aka kawo bayanin Sheikhul Islam Ahmad bn Taimiyya dangane da rinjayar da rashin shar’anta yin addu’a bayan sallame Sallar Farilla!
Allah Ya ba mu dacewa da abin da yake daidai. Wassalamu alaikum wa rahmatullah!