Mai ba Shugaban Kasa Shawara a Kan Harkokin Tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ya yi ganawar sirri da shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati a kan matsalar aikata laifuffuka a intanet.
Wata sanarwa da jami’i mai kula da dabarun sadarwa a Ofishin NSA, Zakari Usman, ya fitar da safiyar Talata, yayin ganawar an tattauna a kan sababbin kalubalen da ke kunno kai a wannan bangaren.
Taron, wanda shi ne irinsa na bakwai, ya kuma tattauna hanyoyin sauƙaƙa da ƙarfafa matakan aiwatar da Manufor Hana Aikata Laififfuka a Intanet ta Kasa ta 2021.
Monguno, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Mashawarta a kan Laifuffukan Intanet, ya koka da yadda bata-gari masu amfani da intanet don aikata laifuffuka ke barnata muhimman na’urorin sadarwa na kasa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar 23 ga watan Fabrairu ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da Manufor Hana Aikata Laififfuka a Intanet ta Kasa.
Mai magana da yawun ofishin na NSA, Zakari Usman, ya bayyana cewa majalisar ta tattauna a kan hanyoyin ba da kariya ga muhimman na’urorin sadarwa na kasa.
Ya kara da cewa, “Ofishin Mai Ba Da Shawara ga Shugaban Kasa a Kan Harkar Tsaro ya yi wa majalisar Karin bayani a kan kare muhimman bayanan kasa kamar yadda aka ayyana a cikin dokar da ta haramta laifuffukan intanet ta shekarar 2015”.