A yayin da ta mallaki karin sabbin tarago, Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya (NRC), ta sanar cewa sabon aikin shimfida layin dogo a birnin Abuja zai fara ne da tashohi goma doriya a kan wadanda ake da su.
Hukumar ta bayyana hakan ne cikin rahoton da ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Laraba. Ta ce jiragen za su rika tsaya wa diba da sauke fasinjoji bayan duk minti talatin.
- Manyan birane 4 da ke fuskantar karancin abinci a Najeriya – NBS
- Gwamnati ta cire hannunta a sanya farashin fetur
Makasudin wannan katafaren aiki shi ne rage cunkoson ababen hawa a titunan babban birnin kasar wanda Gwamnatin Najeriya ta ba da kwangilarsa ga kamfanin gine-gine na China Civil and Construction Company wato CCECC.
A shekarar 2018 ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin tsarin jirgin kasa mai sauki na fasinja da zai rika zirga-zirga tsakanin tashoshi 12 a cikin babban birnin kasar.
Gwamnatin Najeriya ta shafe shekara 11 tana wannan aikin da aka fara tun a shekarar 2007, amma sai a zamanin Shugaba Buhari aka karasa shi.
Hukumomi a Najeriya sun ce tsarin jirgin da zai rika zirga-zirga da fasinjoji cikin sauki, shi ne irin sa na farko a duk Yammacin Afirka.