Hukumar da ke yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi da hana fataucinsu (NDLEA) da ke Jihar Kurosriba ta kama wasu mutane biyu da suka goge wajen sarrafa miyagun kwayoyi da kuma ganyen tabar wiwi a matsayin abincin gwangwani ko kayan makulashe suna sayarwa.
Mutanen biyu, Christian Chindu Joseph, dan shekara 37 da kuma Edet Bassey Edim, dan shekara 30, an kama su a inda suke sarrafa kayan mayen da ke layin Akim Close, Unguwar Akim a Kalaba. Sun shiga hannu ne bayan da aka kyankyasa wa jami’an irin abin da suke yi, inda suka saka kayan a gwangwanin abinci, wanda a zahiri za a ga hakan amma idan an bude babu komai ciki sai kayan maye tsabarsa.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA, Odili Kenneth ya sanar da haka ga Aminiya. Ya ce wadanda ake zargin suna hannunsu ana tsare da su. ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin, yana aiki a wani gidan sayar da kayan lashe-lashe da tande-tande a Fatakwal, ya bari ya dawo Kalaba ya ci gaba da yin irin harkar amma shi yana sanya kayan maye a ciki, yayin da shi kuma Edet Bassey yake kawo masa ganyen tabar wiwi, yana sarrafawa.
Jami’in hukumar ya ci gaba da cewa har wayau hukumarsu ta kama Diyaolu Oluwaseun Dare, dan shekara 27, wanda ya yi safarar hodar Iblis kuma ya zo tashar jiragen ruwa ta Kalaba zai karbi kayan aka kama shi, wanda har ma abokin huldarsa mai suna Dabid Okla James, dan shekara 35 aka bi shi har garin Ugep shi ma aka kama shi.
karin wasu mutanen da hukumar NDLEA a Kurosriba ta ce ta kama, har da wani gurgu a kauyen Iwuru da aka same shi da tarin ganyen tabar wiwi.