Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ce ta kafa dokar gudanar da harkokin Intanet ga masu hada-hada a yanar gizo a matsayin daya daga cikin matakan kare yanar gizo da rage tasirin ayyukan ’yan dandatsa a Najeriya.
Shugaban Hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Dambatta ya bayyana haka a garin Benin da ke Jihar Edo yayin shirin wayar da kan abokan hulda karo na 106 mai taken: “Kawar da tasirin laifuffukan yanar gizo: Rawar da Masu Amfani da Tarho za su taka.”
Mataimakin Daraktan Harkokin Abokan Hulda na Hukumar NCC, Ismaila Adedigba wanda ya wakilci Farfesa Dambatta ya ce yana da muhimmanci a magance yawaitar aikuwar laifuffukan yanar gizo a kasa baki daya musamman a lokacin amfani da Intanet.
Ya ce dokar gudanar da Intanet wani tsari ne na kai-dauki don kare sararin yanar gizon kasar nan daga duk wata barazana ta ’yan dandatsa tare da magance batutuwa kamar kare ’yancin yara da yanar gizo da ’yancin mallaka da kare kunshin data da makamantansu.
Ya bayyana cewa yayin da dokar kai- daukin da sauran dokoki suke tafe don gyara tsarin yanar gizo da masu amfani da tarho, kuma masu amfani da tarho ya zama wajibi su taka muhimmiyar rawa ta hanyar taka-tsantsan da dabarun ’yan damfara.
Da take jawabi, Felicia Onwuegbuchulam, Daraktar Harkokin Abokan Hulda ta bayyana cewa masu amfani da tarho su ne za su ci gajiyar shirin.
“Mun yi imani a matsayinmu na hukuma ba tare da abokan hulda sun fahimci laifuffukan yanar gizo ba, kuma ba tare da kokarin kare na’urorinsu, batagari za su ci gaba da cin karensu ba babbaka a yanar gizo. Sararin yanar gizo ya kunshi dukkan abin da abokin hulda yake yi a yanar gizo da na’urar kwamfuta da suka hada da wayar salula. A yau ’yan kasuwa da daidaikun mutane sun dogara ne da kimiyyar sadarwa wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum inda Intanet ke taka muhimmiyar rawa wajen hada alakar na’urorin da ake amfani da su,” inji ta.
Ta bayyana cewa shirin zai bayyana barazanar ’yan dandatsa ga dukkan masu amfani da tarho tare da ilimantar da su kan rawar da ya kamata su taka domin su kare kansu daga fadawa tarkon ’yan dandatsa da masu aikata laifuffuka a yanar gizo.