Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta bayar da kyautar na’urorin sadarwa ga Cibiyar Nazarin Kimiyya da Muhalli ta Rundunar Sojin Najeriya da ke Makurdi. An mika kayayyakin ne a Abuja a ranar Lahadin da ta gabata don bunkasa bincike.
Kayayyakin sun hada da na’urorin kwamfuta10 da na’urar photocopy mai launi da marar launi da na’urar haska bidiyo daya.
Da yake bayar da kayayyakin, Shugaban Sashen Kimiyyar Sadarwa na Hukumar NCC, Injiniya Abraham Oshadame ya ce sun bayar da kyautar ce saboda bukatar da cibiyar ta mika a watan Oktoban bara, inda ta nemi tallafin hukumar na ba su kayayyakin don amfanin yau da kullum.
“Ina farin cikin sanar da ku cewa hukumar ta yi gaggawar amsa bukatarku ta hanyar bayar da kyautar kayayyakin sadarwar ga cibiyar. Hukumar tana sa ran wannan lamari zai taimaka wa kokarin Rundunar Sojin Najeriya wajen cimma burinta da kuma bunkasa tsaro a kasa. Muna fata wannan tallafi zai yi tasiri ga ma’aikata da dalibai wajen bunkasa iliminsu na kimiyyar sadarwa har ma da bunkasa sha’awarsu ga kimiyyar sadarwa da bunkasa kwarewarsu ta koyarwa da koyo a sauran fannoni. Muna sa ran kayayyakin sadarwar za a yi tattalinsu da kare su tare da kula da su don alfanun ma’aikta da dalibai,” inji shi.
Da yake jawabi, Shugaban Cibiyar, Birgediya Janar, Aminu Abdul wanda Daraktan Kimiyyar Sadarwa na Cibiyar, Misis Chidinma Nwafor ta wakilta ya bayyana godiyarsu ga Hukumar NCC dangane da hadin kan da ta ba su inda suka ci alwashin amfani da kayyakin ta hanyar da ta dace.
Ya ce kayayyakin da aka ba su za su taimaka kwarai da gaske wajen bunkasa bincike da ci gaba saboda cibiyar tana da dalibai da ke nazarin injiniyan na’urar kwamfuta da muhalli.
“A yanzu ba mu da irin wadannan kayayyaki da aka ba mu a dakin bincikenmu da ajujuwanmu. Da wannan babbar kyauta muna da yakinin dalibanmu za su samu kwarin gwiwa su gudanar da bincike mai zurfi da bunkasa,” inji shi.