Hukumar Kwastam ta kama daruruwan hauren giwa da kwanson Pangolin da ake kira dan kunya ko batoyi a wani yanki na Lekki da ke birnin Legas.
Kwanturola Janar na Hukumar, Kanar Hamid Ali mai ritaya ya bayyana hakan yayin yi maname labarai hole kayayyakin da aka kama.
A cewarsa, suna zargin an shigo da kayayyakin ne daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a kokarin fataucinsu zuwa yankin Asiya.
Bayanai sun ce wannan dai shi ne wani kame mafi girma da hukumar kwastam ta yi a Najeriya tun bayan da aka kafa ta, inda darajar kayayyakin ta kai kimanin Naira biliyan 22.3.
An kama Pangolin da nauyinsa ya kai kilogram dubu goma sha bakwai da dari daya da talatin da bakwai a cikin buhuhuna dari daya da casa’in da shida.
Akwai hauren giwa mai nauyin kilogram dari takwas da saba’in, wanda aka kiyasta kudinsu kan dala miliyan 54.
Ya zuwa ya yanzu dai an cafke mutane uku da ake zargi da hannu a harkar fataucin.