Sabon Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi, Mallam Abdulrahman Ibrahim Idris ya fara aiki.
Shugaban ya karbi ragamar hukumar ne a ranar Litinin, yayin wani kwarya-kwaryar biki da ya gudana a hedkwatarta, yana mai alkawarin ba mara da kunya a nauyin da Gwamnan Jihar, Bala Muhammad Bauchi ya dora masa.
Ya bukaci hadin kan shugabanni, ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki a harkar Aikin Hajji da su ba shi dukkan hadin kan da yake bukata don ganin hakarsu ta cimma ruwa.
Tun da farko da yake nasa jawabin, Shugaban hukumar, wanda kuma shi ne Babban Limamin Bauchi, Malam Bala Ahmad Baban-Inna, ya ce Gwamnatin Jihar ta yi zabi mai kyau wajen nadin sabon Babban Sakataren.
Baban-Inna ya ce yana da kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba Jihar Bauchi za ta zama abar misali wajen tafiyar da harkokin Aikin Hajji a Najeriya.
Babban Limamin ya kuma yi wa sabon Babban Sakataren addu’a da fatan samun nasara a aikin da zai fara.
Idan za a iya tunawa, a ranar 14 ga watan Satumban 2021 ce Gwamna Bala Muhammad ya dakatar da Alhaji Abubakar Babangida Tafida daga jan ragamar hukumar, kafin daga bisani ya maye gurbinsa da Malam Abdurahman din.