✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar JAMB da ta NIMASA na fuskantar bincike kan cin hanci

Gwamnatin tarayya ta bayar da ummarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa a Hukumar Kula da Tashar Jiragen Ruwa ta NIMASA da…

Gwamnatin tarayya ta bayar da ummarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa a Hukumar Kula da Tashar Jiragen Ruwa ta NIMASA da kuma Hukumar Da ke Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu ta JAMB.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shi ne ya amince da ummarnin yayin taron majalisar ministocin kasar a jiya.
Ministan Kudi, Kemi Adeosun ita ta bayyana haka ga manema labarai da ke fadar shugaban kasa inda ta bayyana cewa an tafka sata mai yawa a hukumomin biyu.
To amma Ministan ba ta bayyana sunayen mutanen da binciken zai shafa ba kuma ba ta bayyana hukumar da za ta gudanar da binciken ba.