Hukumar Tara Haraji da Hukumar Yaki da Ta’annutin Kudi ta EFCC sun amince su hada gwiwa wajen gano mutane da kamfanoni da suka ki biyan haraji.
Hadin gwiwar zai taimaka wajen kwakulo wadanda ba sa biyan haraji wadanda suka ki yarda su shiga shirin afuwar haraji da gwamnatin tarayya ta bullo da shi da ya nemi su bayyana kadarorin da suka mallaka tare da bayyana kudin shigarsu da ake kira atakaice VAIDS inda ita kuma gwamnatin za ta rage musu dimbin bashin harajin da take bin su.
Tuni har hadin gwiwar tsakanin hukumomin biyu ya kai ga karbo harajin kimanin Naira biliyan 29 da gwamnati take bin bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a kasar a tsakanin watan Nuwamban shekarar 2017 da watan Maris na shekarar 2018.
A taron da ya gudana a yau a hedikwatar hukumar EFCC da ke Abuja, Shugaban Hukumar Tara Haraji, Tunde Fowler ya ce Najeriya kamar kowace kasa a duniya tana neman yadda za ta bunkasa tattalin arzikinta saboda haka ba za ta amince da rashin biyan haraji ba.