Hukumar Tsaro ta DSS ta hana jami’an hukumar yaki da cin hanci da ta’annutin kudi ta EFCC kama tsohon shugaban hukumar, Darakta Janar Ekpenyong Ita.
Aminiya ta gano cewa a ranar Talatar da ta gabata ne jami’an hukumar DSS suka ki yarda jami’an EFCC su kama Ita a gidansa da ke Abuja.
Wata majiya daga EFCC ta fada wa Aminiya cewa Ita wanda shi ne tsohon Darakta Janar na hukumar DSS yana fuskantar bincike a kan zargin satar kudi da karkatar da kudin gwamnati.