✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar DSS ta hana EFCC kama tsohon shugabansu

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta hana jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati  (EFCC) kama wani tsohon Darakta Janar na…

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta hana jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati  (EFCC) kama wani tsohon Darakta Janar na Hukumar DSS, Ekpeyong Ita.

A ranar Talata ne jami’an Hukumar DSS din suka dakile yunkurin jami’an Hukumar EFCC daga kama Ekpeyong Ita a gidansa da ke Abuja. 

Wata majiyar EFCC ta shaida wa Aminiya cewa, Ita, wanda shi ne Darakta Janar na Hukumar DSS na baya-bayan nan, ana bincikarsa kan zarge-zargen laifuffukan da suka shafi sata da karkatar da dukiyar gwamnatin.

Bayanai sun ce, jami’an Hukumar EFCC dauke da waranti kamawa da bincike sun kai farmaki ga Lamba  

46 Mamman Nasir, Asokoro, Abuja, gidan tsohon shugaban Hukumar DSS da misalin karfe 6 na safiyar Talatar, amma jami’an DSS da suke dauke da makamai suka hana su shiga gidan.

Majiyar ta ce, jami’an Hukumar EFCC suna zuwa gidan sai jami’an Hukumar DSS suka kara turo jami’an tsaro kimanin dauke da bindigogi zuwa gidan.

Majiyar ta ce: “Ban sani ba ko yana cikin aikinsu su hana wata hukumar tabbatar da doka kamawa ko bincikar wani gida mallakin wani jami’insu da ya yi ritaya. Mutumin da ake magana a kansa ya daina aiki da Hukumar DSS, wanda hakan ya sa abin da suka yi yake da ban mamaki.”

 Aminiya ba ta samu nasarar jin ta bakin Hukumar DSS ba a hukumance. Hukumar kuma ba ta da mai yin Magana a madadinta balle manema labarai su tuntube shi don neman bayani.

Aminiya ta samu bayanin cewa wani ayarin jami’an EFCC ya ziyarci gidan tsohon Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya (NIA), Mista Ayo Oke da ke kusa da gida Mista Ita.

Shugaba Buhari ya salami Oke daga mukaminsa ne sakamakon badakalar da ta biyo bayan gano sama da Naira biiyan 15 da EFCC ta yi a wani gida da ke Osborne Towers a Ikoyi, Legas. Oke a lokacin ya ce kudin na hukumarsa ce kuma an ajiye kudin ne don gudanar da wasu ayyuka.

A farkon wannan wata Hukumar EFCC ta ce Hukumar DSS ta ki mika mata wadansu ma’aikatanta domin amsa tambayoyi kan binciken da ake yi game da almundahanar sayo makamai.

Kakakin Hukumar EFCC, Wilsob Uwujaren ya ce, ba bakon abu ba ne hukumar ta gayyaci jami’an tsaron da ake zargi da aikata ba daidai ba, su amsa tambayoyi, inda ya ce hukumar ta gayyaci sojojin kasa da na ruwa da na sama kan badakalar sayen makaman, amma sai ga shi Hukumar DSS ta ki amincewa a binciki jami’anta. “Babu shakka binciken badakalar sayo makamai aiki ne na kasa da wadanda ake zargi suka fito daga soja da sauran hukumomin tsaro da kuma ’yan siyasa. Ba ana yi ne don tozarta wata hukuma ba.”