Ma’aikatan sufurin jiragen sama sun yi zanga-zanga a filin jirgi na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Suna kalubalantar shirin Gwamantin Tarayya na damka wa ‘yan kasuwa hudu daga cikin manyan filayen jirgin sama na Gwamnati da kuma neman shigar da su tsarin fansho na hadaka.
Masu zanga-zangar da suka daga kwalaye sun kuma gudanar sallah da addu’o’i na neman Allah Ya hana yiwutar hakan.
Ga wasu daga cikin hotunan yadda zanga-zangar ta kasance: