✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotuna: Yadda wasu Makafi ke sana’ar nika

Wasu magidanta ‘yan uwan juna da Allah ya jarabta da makanta sun bayyana cewa bara kaskanci ne don haka suka   rike sana’ar nika garin albo.…

Wasu magidanta ‘yan uwan juna da Allah ya jarabta da makanta sun bayyana cewa bara kaskanci ne don haka suka   rike sana’ar nika garin albo.

Magidantan uku, masu shekaru daga 60 zuwa 54 mazauna garin Ago-Aare, Jihar Oyo, sun shaida wa Aminiya cewa cutar  makantar ta same su ne a lokacin da suke cika shekaru 30 a rayuwarsu.

Babban su mai suna Muhammadu Sa’adu Isiyaka ya ce kaninsa Sulaiman Isiyaka wanda ke sana’ar dabbobi, shi ne ya sayi injin nika garin alabo wanda yanzu suke amfani da shi a sana’ar da suke dogaro da ita.

Aminiya ta dauko muku hotunan makafin uku da yadda suke sana’ar su ta mika garin albo.