Hotunan matsahin hafsan sojin da ya rasu a hatsarin jirgin Kaduna
Tuni aka yi jana'izarsa bisa tsarin addinin Musulunci.
DagaAminiya
Wed, 20 Apr 2022 7:33:08 GMT+0100
An gano daya daga cikin hafsoshin Sojin Saman Najeriya da suka rasu bayan jirginsu ya yi hatsari a ranar Talata.
Daya daga cikinsu shi ne Abubakar Alkali, dan asalin Jihar Yobe ne, kuma ya kwanta dama ne bayan jirgin da shi da abokin aikinsa suke tukawa ya fadi a Sansanin Sojin Sama da ke Kaduna.
Ga wasu daga cikin hotunan Abubakar wanda tuni aka yi jana’izarsa bisa tsarin Musulunci:
Abubakar Alkali yana daukar kansa hoto a gaban wani jirgin soji.Alkali a lokacin da yake karbar wata kyauta da ya samu saboda jajircewarsa.Marigayi Abubakar Alkali a lokacin wani taro, rike da wata kyauta da ya samu.Abubakar Alkali a kusa da jirgin yaki a wani sansanin soji, a lokacin rayuwarsa.Shi ne a nan a lokacin wani faretin daurin auren wani abokin aikinsu.Abubakar a cikin fararen kaya a wani filin jirgin sama a lokacin rayuwarsa.