✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

HOTUNA: Ziyarar Sarkin Kano Marrakesh ta Kasar Morocco

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, ya ziyarci kasar Morocco a bisa gayyata ta musamman don halartar bikin al’adun gargajiya na wasan dawakai na…

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, ya ziyarci kasar Morocco a bisa gayyata ta musamman don halartar bikin al’adun gargajiya na wasan dawakai na shekara – shekara da ake yi.

An kuma mai martaba sarkin kyautar yabo ta bikin

Sarkin ya gana Ministan kula da Al’adun Gargjiya da Matasa, sannan ya kuma je ganin sabbin jiragen saman AA Rano da ke kasar a in da ya gana da ma’aikatan kamfanin.

Ana sa rai sarkin zai dawo kasar nan a ranara Asabara 22 ga wtan Oktoba 2022

Ga yadda ta kasance a cikin hotuna:

Sarkin Kano tare da Ministan Al’adu da Matasa na Morocco, Mehdi Bensaid da Jami’in Najeriya a Maroko (Hoto: Ayarin sarki).
Mai Martaba Sarakin Kano tare da Ministan Al’adu na Maroko, Mehdi ben Said da ’yan rakiyar Sarki (Hoto: Ayarin Sarkin Kano a Maroko).
An ba Sarkin na Kano kyautar yabo na halartar bikin al’adun garagajiya na dawakai na shekarar 2022 (Hoto: Danmorin sarkin Kano/Isa Pilot).
Isowar Sarkin Kano wurin liyafar cin abinci inda aka karrama shi a taron kammala bikin (Hoto: Ayarin Sarkin Kano a Maroko).
Sarkin Kano tare da wasu ma’aikatan kamfanin jirgin sama na AA Rano yayin da sarkin ya kai ziyarar ganin jiragen a Maroko. (Hoto: Ayarin Sarkin Kano a Maroko).
Sarkin Kano yayin da ya shiga cikin jirgin don sa albarka (Hoto: Ayarin Sarkin Kano a Maroko).
Sarki tare da Isa Pilot a cikin jirgin A.A Rano yana sa albarka. (Hoto: Ayarin Sarkin Kano a Maroko)
Sarkin Kano da jama’arsa da kuma wasu daga cikin jami’an kamfanin jiragen A.A Rano na marhabin da sarkin (Hoto: Ayarin Sarkin Kano a Maroko).
Wasu daga cikin ayarin sarki a daya daga cikin bukukuwan da aka shirya a kasar (Hoto: Ayarin Sarkin Kano a Maroko)
Sarkin Kano a yayin kallon wasu daga cikin bukukuwan da aka shirya a kasar. (Hoto: Ayarin Sarkin Kano a Maroko).
‘Yan Najeriya mahaya dawakai cikin shigar garagajiya na nuna al’adar Masarautar Kano a hawan dawakai. (Hoto: Ayarin Sarkin Kano a Maroko)
Mai martaba sarki da wasu daga cikin ’yar rakiyarsa a wajen bikin hawan dawakai a kasar (Hoto: Ayarin Sarkin Kano a Maroko)