Zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal.
Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta.
- Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC
- Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno
A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare haƙƙin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunƙurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi
An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu ɗauke da rubutun bayyana buƙatunsu a wasu hanyoyi da ke Ikeja, babban birnin Jihar Legas.
A Jihar Ribas kuma, masu zanga-zangar sun yi dandazo a filin Isaac Boro da ke birnin Fatakwal, amma dai ’yan sanda sun riƙa harba musu barkonon tsohuwa domin daƙile manufar da suka fito ita.
Aminiya ta ruwaito Ƙungiyar ta Take It Back na cewa zanga-zangar da za gudanar a yau babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gargaɗi masu shirin zanga-zangar a ranar Litinin 7 ga watan Afrilu a faɗin ƙasar su sake tunani domin a ranar ce ‘yan sandan ƙasar suke bukukuwa domin nuna gudunmawar da suka bayar don ci-gaban Nijeriya.
Rundunar ta ce zanga-zangar tana zuwa ne a lokacin da bai dace a yi zanga-zanga a ƙasar ba.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce rundunar ba ta adawa da ‘yancin ‘yan ƙasar na taruwa da yin gangami da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba su.
Sai dai kuma sanarwar ta ce rundunar na fargaba game da burin waɗanda suka shirya yin zanga-zangar rana ɗaya da ranar da aka ware domin yaba wa irin jajircewa da sadaukar da kai na ‘yan sandan Nijeriya.
“Bisa ga ingatattun ɗabi’un da ƙasashen duniya ke bi wajen yabawa da nasarorin ‘yan sandansu, gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakin ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sandan Nijeriya,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa bikin zai samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar daga fannoni daban-daban, ciki har da sufeto janar na ‘yan sandan ƙasashen ƙetare da kuma jami’an diflomasiyya.
“Dalilin gudanar da zanga-zanga a irin wannan ranar abin dubawa ne kuma a iya cewa wani mataki ne na ɓata sunan ‘yan sandan Nijeriya da ƙasar ma baki ɗaya,” in ji sanarwar.
“Saboda haka rundunar ‘yan sandan Nijeriya tana bai wa waɗanda suka shirya wannan zanga-zangar shawarar janyeta saboda lokacin bai dace da ita ba kuma tana da manufar aikata ɓarna,” in ji Olumuyiwa.
Dalilin da za mu yi zanga-zanga — Take It Back
Sai dai duk da wannan gargaɗi, ƙungiyar ta Take It Back ta ce tana nan kan bakarta domin nuna adawa kan abin da ta kira mulkin kama karya da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi a ƙasar nan.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a ƙarshen mako, jagoran ƙungiyar, Juwon Sanyaolu, ta ce za su gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar domin nuna adawa da rashin shugabanci nagari da kuma daƙile ’yancin faɗar albarkacin baki.
Ga wasu hotunan yadda zanga-zangar ke gudana: