Kananan da matsakaitan ’yan kasuwa a Rukunin Masana’antu da ke Dakata a Kano sun yi sallah da addu’o’i domin neman dauki daga Allah, bayan rashin wutar lantarki na kwana 70.
Ana hasashen sama da mutum 10,000 ne ake jin lamarin ya shafa baya ga asarar miliyoyin kudade.