✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda Tinubu da Ɗangote suka yi Babbar Sallar a Legas

Tinubu ya gudanar da sallar Idin tare da wasu hadimansa a Legas.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da Sallar Idi tare da wasu manyan hadimansa da abokansa a Jihar Legas.

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, attajirin Afirka, Aliko Dangote; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, na daga cikin waɗanda suka halarci sallar tare da shugaban ƙasa.

Ragowar sun haɗa da tsohon ministan wutar lantarki, Babatunde Fashola, mataimakin gwamnan Jihar Legas, Obafemi Hamzat, tare da tsohon ministan tsaro, Sanata Musiliu Obanikoro.

Ga hotunan yadda sallar ta gudana a ƙasa: