Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya ziyarci Jihar Kano, inda ya yi buda baki tare da al’ummar Musulmi a jihar.
Obi, ya ziyarci Masallacin Sheikh Jibril Umar Jibril wanda aka fi sani da Triumph da ke Karamar Hukumar Fagge a jihar.
- Matsalar Tsaro: Jami’an tsaro sun gayyaci Sheikh Gumi — Gwamnati
- Mazauna karkara na neman daukin ruwan sha a Gombe
Dan takarar shugaban kasar, ya shafe mintuna a masallacin bayan yin buda baki.
Ya ce: “Na zo ne domin yin buda baki tare da ku kuma ina farin cikin kasancewa a nan, na zo ba tare da nuna wariya ko la’akari da addini ko kabila ba.
“Ina fatan addu’o’in da muka yi a wannan wata na Ramadan mai albarka Ubangiji zai amsa mana, dukkaninmu ’yan Najeriya ne, kuma al’umma daya, na yi imani dole ne mu yi wa kasarmu addu’a.”
Tun da farko, Obi ya ziyarci Fadar Sarkin Kano, domin taya Sarkin da daukacin al’ummar jihar murnar fara azumin watan Ramadan.
Ga hotunan yadda ɗan takarar ya yi buda baki da Musulmai a jihar: