✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda ake fama da ƙarancin man fetur a Abuja

A kwanakin baya matsalar man fetur ta sanya farashin litar ta kai Naira 800 zuwa sama da N1,000.

Matsalar ƙarancin man fetur ta sake kunno kai yayin da aka wayi gari yau Juma’a dogayen layukan ababen hawa sun mamaye gidajen mai a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Wannan na zuwa ne ‘yan watanni bayan da ‘yan Najeriya suka fuskanci matsalar man fetur da har farashin litar ya kai Naira 800 zuwa sama da N1,000 a wurin ’yan cuwa-cuwa da masu bumburutu.

Tun bayan cire tallafin man fetur ’yan Najeriya ke fuskantar tsadar rayuwa tare da tsadar sufuri da kuma hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka.

Ga wasu hotunan yadda dogayen layukan suka mamaye gidajen mai a Babban Birnin Nijeriya: