✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

HOTUNA: Yadda aka yi hawan Daushe a masarautar Kano da Bichi

A ranar Lahadi ce Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da dan uwansa Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero suka gudanar da hawan Daushe a bisa al’ada…

A ranar Lahadi ce Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da dan uwansa Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero suka gudanar da hawan Daushe a bisa al’ada ranar daya ga Sallah.

Ga yadda hawan ya gudana a Bichi da kuma cikin birnin Kano a inda manyan mutane daga ciki da kuma wajen kasar suka halarta.

Bisa al’ada sarki na fitowa ne bayan la’asar shi da mutanensa, inda yake kewayawa wasu sassa na garin Kano, kuma jama’a na fitowa su yi jinjina da kuma gaisuwa ga sarki.