A ranar Lahadi ce Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da dan uwansa Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero suka gudanar da hawan Daushe a bisa al’ada ranar daya ga Sallah.
Ga yadda hawan ya gudana a Bichi da kuma cikin birnin Kano a inda manyan mutane daga ciki da kuma wajen kasar suka halarta.
- NAJERIYA A YAU: Yadda aka saki fasinjoji 7 na jirgin kasan Abuja-Kaduna
- Dalilin da ban zabi Kirista a matsayin abokin takara ba —Tinubu
Bisa al’ada sarki na fitowa ne bayan la’asar shi da mutanensa, inda yake kewayawa wasu sassa na garin Kano, kuma jama’a na fitowa su yi jinjina da kuma gaisuwa ga sarki.