A wannan Larabar 15 ga watan Janairu ake bikin Ranar Tuna wa da Mazan Jiya ta bana a faɗin Nijeriya.
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ne ya wakilci Shugaba Bola Tinubu wanda ke halartar taron cigaba mai dorewa a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa, a bikin.
- Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana
- An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo
A yayin bikin na yau da ya gudana a dandalin taro na Eagle Square, Sanata Kashim Shettima ya ajiye furen girmamawa domin tuna wa da sojojin ƙasar da suka rasa rayuwarsu a ƙoƙarin kare Najeriya.
Baya ga Kashim Shettima, sauran mambobin majalisar ministocin Tinubu sun halarci bikin domin karrama dakarun da suka kwanta dama da iyalansu ta hanyar dora furan kallo, da gudanar da sauran al’adun soja ciki har da harba bindigogi sama.
Tsoffin sojoji ne dai ke bikin wannan rana a duk shekara domin tuna wa da ƴan uwansu da suka bayar da rayuwarsu wajen kare ƙasa, inda ake gudanar da bikin a tarayya da jihohi da kuma matakin ƙananan hukumomi.
Baya ga ɗora furen bangirma da shugabannin ke yi, ana kuma yin faretin bangirma da sojojin ƙasa da na sama da na ruwa ke haɗuwa su yi.
Kowacce ranar 15 ga watan Janairu, rana ce da gwamnatin Najeriya ke gudanar da gangami na musamman don tunawa da tarin sojojin da suka rasa rayukansu a fagen yaƙi, ranar da ake yi wa laƙabi da ranar tunawa da ‘yan mazan jiya wato Armed Forces Remembrance Day.
A baya dai Najeriya na gudanar da wannan biki ne a ranar 11 ga watan Nuwamban kowace shekara tare da sauran ƙasashen duniya a matsayin ranar bikin murnar kawo ƙarshen yaƙin duniya na I.
To amma tun bayan da Gwamnatin Nijeriya ta samu nasara kan mayaƙan aware na Biafra a ranar 15 ga watan Janairun 1970, sai aka mayar da ranar bikin tuna wa da mazan jiya zuwa watan na Janairu domin tuna wa da yaƙin da ya so ya tarwatsa ƙasar.