✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya

Obi ya yaba da irin gudunmawar da Ɗantata ya bayar wajen bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ziyarci iyalin marigayi, Alhaji Aminu Dantata a Jihar Kano, don yi musu ta’aziyya.

Obi, ya bayyana cewa ya yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar Alhaji Ɗantata, inda ya bayyana shi a matsayin “uba ga kowa.”

Ya yaba yadda Ɗantata ya zama babban attajiri kuma ya taimaka wa mutane da dama suka samu nasara a rayuwarsu.

Ya ce Ɗantata ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya.

“Mun zo nan yau don jimami tare da iyalinsa da kuma ɗaukacin ‘yan Najeriya, saboda wannan babban rashi ne,” in ji Obi.

“Alhaji Aminu Dantata ba mai kuɗi ba ne kawai, ya taimaka wa wasu wajen cimma nasararsu a rayuwa.

“Ya kula da mutane sosai kuma ya zama kamar uba ga mutane da dama.”

Obi, ya bayyana Ɗantata a matsayin mutum mai tausayi da kishin ƙasa.

Ya ce mutuwarsa ta shafu al’amura da dama a wannan zamani.

Haka kuma, Obi ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya saka masa da alheri, ya kuma albarkaci iyalinsa.

“Rayuwarsa abin koyi ce. Ba wai kasuwanci kawai ya yi ba, ya zuba jari a cikin al’umma. Abin da ya bari zai ci gaba da zama abin koyi.

“Allah Ya albarkaci wannan gida, ya albarkaci Najeriya baki ɗaya,” in ji Obi.

Alhaji Aminu Ɗantata fitaccen ɗan kasuwa ne luma mai taimakon jama’a daga Arewacin Najeriya.

Ya rasu yana da shekarau 94.

Mutane da dama daga sassa daban-daban na ƙasar nan sun yi alhini bisa gudunmawar da ya bayar a harkar tattalin arziƙi da taimakon jama’a.

Ga hotunan ziyarar a ƙasa: