✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Jama’a sun koka kan yadda gwamnati ke rusau a Abuja

Hukumar Tsara Birnin Tarayya (FCTA), ta lashi takobin daidaita Abuja.

Mazauna unguwar Daki Biyu da ke yankin Jabi a Birnin Tarayya Abuja, sun shiga firgici sakamakon yadda hukumomi ke ci gaba da rusa matsugunansu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Hukumar Tsara Birnin Tarayya (FCTA) ta lashi takobin ci gaba da dawo da birnin kan tsarin da aka kafa shi.

‘Yan jari bola na kwasan abin da ya yi saura bayan rusau da hukumar ta yi a unguwar Daki Biyu.
Tulin fallayen kwano da ‘yan jari bola suka tara bayan rusau da gwamnati ta yi a unguwar Daki Biyu da ke Abuja.

Wasu daga cikin wadanda rusau din ya shafa suna kwashe kayayyakinsu da suka yi saura