Aikin Hajjin shekarar 20 ya zo da abubwa da dama da ba saba gani ba tsawon shekarun ibadar, wadda miliyoyin Musulmi daga fadin sassan duniya ke taruwa a Kasar Saudiyya domin gudanarwa.
Bullar cutar coronavirus ta takaittta mahajjata zuwa mutum 10,000 tare da tsaurara matakan kariya a lokacin ibadar.
Ga wasu hotuna Ranar Arfa ta 1441 Hijiriyya, wadda ta yi daidai da Alhamis 30 ga Yuli 2020 Mildaiyya.
Masallacin Namirah inda alhazai ke yin sallolin Azahar da La’asar a hade cikin jam’i bayan sauraron huduba ya kasance tamkar babu mutane saboda karancin alhazai a banaIsowar wani rukuni na alhazai a Masallacin Namirah daga Mina a safiyar ranar ArfahKowane mahajjaci ya dukufa da ibada a ranar da ta fi kowacce a ranakun aikin Hajji
Kankan da kai irin na bawa a gaban Mahaliccinsa yayin da baiwar Allan nan ke ibadaShaikh Abdullah Manea, limamin ya yi huduba ya kuma jarorancin sallar Azahar da La’asarZaman tahiya a lokacin sallar jam’i a ranar ArfahWata daga cikin hajiyoyi tana shafa addu’a bayan ta kammala a ranar Arfah.Alhazai da ma’aikata a lokacin da ake hada jam’in sallolin Azahar da La’asar a ranar ArfahWani daga cikin alhazai yana yin addu’a a Ranar Arfah a cikin masallaciMahajjahta sun dukufa wajen yin addu’o’i a zikirori a Ranar ArfahMahajjata na shirin jiran huduba kafin sallolin farilla da a masallacin Namira a filin Arfah