Shirye-shiryen bude masallatai da majami’u sun fara kankama a jihar Legas a daidai lokacin da ake ci gaba da yi wa wuraren ibadar rijiasta.
Hakazalika an soma yi wa wuraren ibadar feshin magani duk a cikin shirin gwamnatin Legas na bude masallatan a ranar 19 ga watan Yuni, yayin da za a bude mujami’ai a ranar 21 ga wata Yuni.
Ga dai hotunan yadda aka yi feshin Masallacin Alhaja, wato babban masallacin juma’a na ‘yan Arewa mazauna Legas, masallacin da al’umar Arewa suka fara mallaka a Legas.
An yi wa masallacin feshin an kuma rushe rumfunan da ke kewaye da shi, wadanda a baya ‘yan kasuwa ke amfani da su wajen gudanar da cinikayya, duk a kokarin gwamnatin na rage cunkoso a daura da masallacin domin kare yaduwar annobar coronavirus.