Manyan ’yan siyasa a Najeriya na ci gaba da sauka a Jihar Kano domin halartar ɗaurin auren ’yar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ɗan fitaccen attajiri, Dahiru Mangal.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, na daga cikin manyan ’yan siyasar da yanzu haka sun sauka a Birnin Dabo.
Aminiya ta ruwaito cewa, a wannan Asabar ce za a ɗaura auren Dokta Aisha Rabiu Musa Kwankwaso da angonta, Injiniya Fahad Dahiru Mangal.
Daga cikin tsofaffin gwamnonin da ke halartar bikin akwai Ahmed Makarfi na Jihar Kaduna da Abdulaziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara da Isa Yuguda na Jihar Bauchi da Adamu Aliero na Jihar Kebbi.
Sauran tsofaffin gwamnonin sun haɗa da Lucky Igbinedion na Jihar Edo da Mahmud Shinkafi na Jihar Zamfara da Victor Attah na Jihar Akwa Ibom.
Bayanai sun ce ɗaurin auren dai ya zama tamkar wani taron sake saduwa bayan shekaru tsakanin manyan ’yan siyasar Najeriya.