Akalla mutane 18,059, ciki har da yara kanana 795 masu cutar AIDS ne suke karbar magani a Jihar Borno.
Babbar Sakatariyar Hukumar Yaki da Cutar AIDS ta Jihar Borno (BOSACA), Falmata Alhaji-Bukar, ta ce cutar na kara karuwa a jihar, kuma hukumar za ta kara wayar da kan jama’a kan cutar, musamman a yankunan karkara.
A cewarta, mazauna birane sun fi fahimtar abin da za su yi game da cutar AIDS, ba kamar na yankunan karkara ba.
“Don haka ne bayan shirin da aka gabatar na ranar yaki da cutar a Maiduguri, za mu wuce karamar hukumar Mafa mu sake gudanar da shirin fadakarwar.
Ta jaddada bukatar da mutane su san matsayinsu da muhimman matakan yakar cutar
A cewar ta, hukumar tare da hadin guiwar ma’aikatar lafiya da wasu abokan huldarta, sun shirya wajen yaki da cuta har sai sun ga bayanta Kuma duk mai dauke da cuta ba tare da ya sani ba, za su yi kokarin kawo masa dauki ya samu sauki in Allah ya so.
Sakataren zartaswar na hukumar, Mamman Musa ya bayyana rashin tsaro a wasu yankunan da karancin ma’aikata a matsayin manyan kalubalen yaki da cutar a jihar.
“Muna fatan ma’aikatar za ta yi wani abu game da daukar karin ma’aikata.”
Har ila yau, Malam Mamman Musa, wani mai fama da cutar a Borno, ya bukaci karin tallafi da kudade don yaki da ita.
Ya bukaci gwamnati da ta tallafa musu da ofis don ba su damar bayar da gudummawa yadda ya kamata a yakin da hukumar ke yi da sauran batutuwa.
“Muna kuma bukatar motar daukar marasa lafiya domin daukar wasu mambobinmu musamman wadanda ba za su iya tafiya zuwa karbar magani ba saboda illar da wannan cuta ke musu” in ji Musa.