✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hisbah za ta kara yawan ofisoshinta a Kano

Hisbah ta ce za ta kara yawan ofisoshinta ke don yaki da bata-gari a jihar.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta samu sahalewar Gwamnatin jihar domin fadada yawan ofisoshinta a jihar.

Babban Kwamandan hukumar, Harun Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara ofishin hukumar dake rukunin gidaje na Sheikh Nasiru Kabara, wanda aka fi sani da (Amana).

Babban Kwamandan ya ce, “Shirye-shirye sun yi nisa wajen fadada yawan ofisoshinmu kuma a sabuwar shekarar nan da karfinmu za mu dawo aiki.

“Abubuwa suna tafiya yadda ya kamata, kuma za mu tabbatar da an gina ofis a sabbin unguwannin Kano, don yaki da bata gari,” cewar Ibn Sina.

Ya kara da cewa, za a tabbatar da gina karin ofisoshinta a dukkan lungu da sako na jihar.

A cewarsa, ta haka ne kawai hukumar za ta samu saukin yaki da bata-gari a jihar.