Hukumar Hisbah ta Jihar Kano a ranar Laraba ta jagoranci fasa giya fiye da kwalba miliyan biyu da ta kwace a fadin Jihar.
An gudanar da aikin ne a garin Hawan Kwalabawa da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa da ke Jihar, bisa jagorancin Babban Kwamandan Hukumar hukumar, Sheikh Muhammad Sani Ibn Sina.
- Gawuna ya taya Abba Gida-Gida murnar lashe zaben Gwamnan Kano
- Da wuka na yi amfani wajen kisan Ummita – Dan China
Da yake yi wa Aminiya karin haske game da aikin, Babban Kwamandan na Hisbah ya ce giyar da aka lalata an kama ta ne a manyan titunan Jihar da kuma wasu wuraren shan ta.
“Yawancin giyar da muka lalata mun kama ta ne a kan manyan titunan Jihar a daidai lokacin da masu ita ke kokarin shigowa da ita cikin Jihar.
“Abin da muke yi shi ne muna datse giyar ce a kan hanyar shigo da ita Jihar wato ba mu bari ta kai ga shiga cikin gari ballantana a kai ga raba ta a wuraren sayarwa,” inji shi.
Babban Kwamandan ya bayyana cewa, “Muna gudanar da wannan aiki ne ta hanyar bin hukuncin kotu. Kasancewar muna da dokarmu da ta ba mu damar kama kayan maye a fadin Jihar Kano Dokar ta haramta shigo da giya da rarraba ta da kasuwancinta da kuma shanta a fuk fadin jihar Kano. A takaice haramun ne yin ta’mmali da giya ta kowacce fuska a Jihar Kano,” in ji Ibn Sina.
Ya kuma ce duk abin da suke yi na lalata giya suna yi ne bisa doka.
“Idan muka kama irin wadannan kaya muna kai wa kotu. Ita kuma za ta ci tarar masu kayan, sannan za mu nemi izininta kan ta ba mu damar lalata giyar, idan muka samu sahalaewar kotu sai mu dauki kayan mu je mu farfasa tare da kona su,” in ji shi.