✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hisbah ta kama tirela makare da kwalbar giya 18,000 a Kano

Hisbah ta ce ta kama motar ne a Gwarzo, tana kokarin shiga Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama wata tirela makare da giyar da ake kokarin shiga da ita jihar.

An kama motar ne dauke da kiras 1,500, wato kimanin kwalba 18,000 ranar Lahadi a kan hanyar Gwarzo zuwa Kano.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da sashen yada labaranta ya fitar ranar Litinin, dauke da sa hannun Babban Kwamandanta, Harun Muhammad Ibn Sina.

Sanarwar ta ambato Babban Kwamandan na cewa, “Wannan motar gaba dayanta giya ce. Kuma irinta muna da kusan tirela 10. ba don aikin da Hisbah ta yi na kama ta ba, da duk a Kano za a shanye ta.

“Ya kamata jama’a su san cewa har yanzu sayarwa, rabawa, dakon giya haramun ne a jihar Kano, kuma duk inda muka gan ta za mu kama. Kuma nan da lokaci kadan za mu yi bikin farfasata,” inji Ibn Sina.