Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu motoci makare da giya har katon 5,760 a kan titin Kano zuwa Madobi.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ya fitar, Lawan Ibrahim Fagge, a ranar Alhamis.
Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Harun Muhammad Sani Ibn-Sina, ya ce an samu nasarar cafke motocin biyu ne bayan samu bayanan sirri daga wasu mutane na gari.
Ya kara da cewa hukumar za ta fara bincike don daukar matakin da dace da kuma ci gaba da yaki da sha da kuma fataucin kayen maye a tsakanin matasa a fadin Jihar.
Kazalika, ya yaba wa dakarun hukumar, ’yan sa-kai da masu ruwa da tsaki a jihar kan yadda suke taimakon hukumar, yana mai cewa shaye-shaye a tsakanin matasa ya zama babbar matsala.
Babban Kwamandan, ya kara da cewar hukumar za ta ci gaba da fadada kawance da wasu hukumomin don yaki da dabi’ar ta’ammali da kayan maye.
A wani labarin kuma, hukumar ta Hisbah ta sake cafke matasa, samari da ’yan mata sama da 100, a yayin wani samame a titin Abdullahi Bayero da kuma titin gidan Zoo.
Babban Kwamandan hukumar ya bayyana damuwa kan yadda ake samun matasa ciki har da ’yan kasa da shekara 15 suna shan shisha da sauran kayan maye.
Wasu daga cikin wadanda aka cafke din, yayin zantawa da Aminiya sun roki da a yi musu afuwa tare da daukar alkawarin ba za su sake aikata laifin da ake tuhumarsu da shi ba.